1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru talatin da aukuwar tarzomar unguwar Soweto

June 16, 2006
https://p.dw.com/p/Butl
Kasar Afirka Ta Kudu na gudanar da bukukuwan cika shekaru 30 da aukuwar hargitsin nan da ake yiwa lakabi da tarzomar Soweto na nuna adawa da mulkin nuna wariyar launin fata. Shugaba Thabo Mbeki ya jagoranci wani jerin gwano da aka yi yau a Soweto, sannan daga bisani ya yi jawabi a gaban mutane sama da dubu 40 a babban filin wasan kwallon kafa na Soweto. Shugaba Mbeki yayi kira ga matasan na yanzu da su guji aikata laifuka kana kuma su yaki cin hanci da rashawa kamar yadda takwarorinsu a wancan lokaci suka yaki mulkin nuna wariya. Alkalumman da ´yan sanda suka bayar sun nunar da cewa mutane 575 suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da aka yi ta yi tun daga 16 ga watan yunin shekara 1975 zuwa watan fabrairun shekara ta 1977, amma alkalumman da ba na hukuma sun ce wadanda aka halaka sun fi haka yawa. An fara tarzomar ne bayan da ´yan sanda suka bude wuta akan yaran makaranta dake zanga-zangar nuna adawa da shirin gwamnati na koyar da harshen Afrikan, wanda ya kasance yaren tsiraru fararen fata ´yan mulkin nuna wariya a ATK.