1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shelar Al-Qa'ida ta hallaka bafaranshe

July 26, 2010

Reshen ƙungiyar Al-Qa'ida na yankin arewacin Afirka yayi iƙirarin kashe Michel Germano da ya ke garkuwa da shi.

https://p.dw.com/p/OUXN
Usama Bin LadenHoto: AP

Reshen ƙungiyar Al-Qa'ida na yankin arewacin Afirka yayi shelar hallaka wani bafaranshe da ya shafe watanni uku ya na garkuwa da shi a hamadar ƙasar Mali da Mauritaniya. Dama reshen ƙungiyar ya ƙayyade ma gwamantin Faransa wa'adin watannin uku domin ta biya ma shi bukatun da ya miƙa mata, ko kuma ya hallaka Michel Gerrmano, wani jami'in sa kai da ya sace a kan iyakar Jamhuriyar Niger da kuma Mali.

Gwamantin Faransa ba ta tabbatar da sahihancin labarin ba har ya zuwa yanzu. Amma kuma shugabanta wato Nocolas Sarkozy zai gudanar da wani taron gaggawa a wannan litinin da ministocin da ke kula da harkokin tsaro na ƙasar, domin abin da ya kira ɗaukan matakan da suka wajaba. Sojojin ƙundunbalar Faransa sun yi ma 'yan takifen na Al-Qa'ida dirar miƙewa a maɓuyarsu da ke ƙasar Mauritaniya a makon da ya gabata, ba tare da nasarar ceto shi Michel Germano mai shekaru 78 da haihuwa ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal