1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shigar Turquia a Ƙungiyar EU ?

June 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuuF

Tun jiya litinin a ka fara tantanawa tsakanin EU, da ƙasashen Turquia da Crotia, wanda su ka ajje takara.

Bayan wata, da watani, na taƙƙadama a dalili da adawar Sypros, ministocin wajen EU, sun fara tantanawa, a game da matakin farko, daga jerin matakai 35 na karɓar Turquia a sahun ƙasashen EU.

Komishinan EU mai kula da faɗaɗa wannan ƙungiyar ya ce fara tannawa da Turquia ,na matsayin wani babban ci gaba, na dangata tsakin ɓangarorin 2.

Saidai a wani sashen kuma, ministocin harakokin wajen EU, sun rattaba hannu a kann wani daftari, mai kira ga hukumomin Ankara, da su ƙara inganta hulɗoɗi tsakanin su da ƙasar Syprus, da ta zama member a EU, a shekara da ta gabata.

A ɓangaren ƙasar Ƙroshia, ƙasahen EU, na kauttata zaton ba a za a samu wata doguwar matsala ba, idan a ka kwatanta da Turquia.