1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Mata a masana'atar shirya fim ta Kannywood

Ramatu Garba Baba MNA
July 8, 2019

A wannan makon shirin ya yada zango ne a masana'antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood da ke Kanon Najeriya. Kannywood dai ta shahara a fannin shirya fina-finai masu kayatar da nishadantarwa.

https://p.dw.com/p/3LkOb

A yayin da matasa da dama ke yabawa da irin nishadin da suke samu daga salon raye-raye da kade-kade da fina-finan Hausa ke zuwa da su, wasu daga cikin al'umma na adawa da fina-finai na Hausa da suka ce na kokarin gurbata tarbiyya musamman ta yara da matasa.

Batun bai tsaya nan ba don kuwa su kansu jarumai musamman mata na shan suka, inda ake musu kallon 'yan nanaye da ba su san ciwon kansu ba.

Shin me ke janyo zarge-zarge da suka? Wadanne irin kalubale masana'antar ke fuskanta? Shin akwai bambancin a sana'ar fim da sauran ayyuka da mata ke yi? Mai ya sa duk da wadannan zarge-zargen mata ke kara sha'awar shiga harkar ta fim?

Akwai amsa da ma karin bayani a cikin shirin.