1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin bikin Kirsimeti a jihar Agadez

December 20, 2022

Baki da ke zaune a Jihar Agades a arewacin Nijar na shirye-shirye bukukuwan Kirismeti, sai dai ba tare da iyalensu ba, sakamakon yadda suka baro gidajensu a kan hanyarsu ta zuwa cirani

https://p.dw.com/p/4LFLJ

Jihar Agadez da ke arewacin Niger, jiha ce da ta kasance magama ta shige da ficen baki masu son zuwa cirani kasashen Turai da suka yada zango Agadez don neman kudi kafin su koma kasashensu bayan sun gwada tafiya don neman rayuwa mai kyau. Sai dai a cewar Anna Ayoni da ya fito daga Nigeria cewa yayi gaskia a wanan lokaci na Shirye Shiryen Kirismeti yana tuna irin haduwa da zumunci da suke yi tare da 'yan uwansu daga wasu kasashe

Akwai kungiyoyi kamar OIM, HCR da ke taimaka wa bakin ta hanyar dafa musu abinci mai dadi da kuma abin sha inda suke haduwa su yi zumunci a tsakaninsu.