1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin bunƙasa tattalin arzikin yankin yammacin Afirka

November 23, 2012

Ƙarfafa hulɗa tsakanin kungiyar Tarrayar Turai da man'yan ƙungiyoyi na yankin yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/16p0j
Leaders and representatives from regional group Economic Community of West African States (ECOWAS) attend a meeting in Yamoussoukro June 29, 2012. REUTERS/Thierry Gouegnon (IVORY COAST - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta yamma wato Ecowas da hukumar kula da harkokin kuɗi ta ƙasashen yammacin Afrika ta UEOMOA sun cimma yarjejeniyar tsara aiyyukan da asusun gudanar da ci gaba na ƙungiyar Tarayyar Turai ke ɗaukan nauyi a ƙasashen ƙungiyar, ta yadda za'a aiwatar da su bai daya , a matsayin hanyar ƙara samun ƙawance da ci gaban al'ummomin su.

Tun dai daga shekara ta 2004 ne hukumomin biyu na Ecowas da Uemoa suke aiki tare domin ƙara samun bunƙasar tattalin arzikin yanki ta hanyar sa ido a kan aiyukan ci gaban da ake gudanarwa a ƙasashe 16 da ke cikin ƙungiyar ta Ecowas, wannan ya sanya shugabanin hukumomin biyu gudanar da muhimmin taro a Abuja, inda suka yi nazari tare da cimma yarjejeniya a kan aiyyukan tallafin da asusun gudanar da aiyukan ci gaba na ƙungiyar Tarryar Turai ke aiwatar wa a ƙasashen.

Ƙaddamar da tsarin tattalin arziki bai ɗaya na ƙasashen yankin yammacin Afirka

Shugaban ƙungiyar ta Ecowas Mr Kadre Desire Ouedraogo ya bayyana muhimmancin samun gudanar da aiyyukan su kasance bai ɗaya a tsakanin hukumomin biyu duk da cewa Ueomoa na daga ƙasashen da ke cikin ƙungiyar Ecowas ne.

General picture of an ECOWAS Summit gathering west African leaders to plot a military strategy to wrest control of northern Mali from Islamist groups as fears grow over the risks they pose to the region and beyond, on November 11, 2012 in Abuja. West African plans could see the mobilisation of some 5,500 soldiers, essentially but not totally drawn from the region. Between 200 and 400 European soldiers will train troops in Mali, according to the operational plan. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Yace ‘'An tsara shirye-shiyenmu ne a dukanin ƙasashe goma sha biyar da ke ƙungiyar Ecowas don haka akwai buƙatar ganin ana aiwatar das u tare ta yadda yake a ko wane lokaci zamu tabbatar da cewar Afirka ta yamma na amfana da waɗannan aiyyuka ta hanyar samun shiri ɗaya ne kuma aiki guda don haka mun dade muna aiki tare ''.

Asusun gudanar da aiyyukan ci gaban na tarrayar Turai ya kasance mai taimaka samar da kudaɗen gudanar da aiyukan ci gaba ga ƙasashen ƙungiyar musamman ma dai a fanin aikin gona da ka iya zaburara da tattalin arzikin yanki. To ko wane tasiri kai tsaye aka gani zahiri a ƙasashen ganin kasashe na goma da na sha daya ake Magana a yanzu? Mr Cheikhe Hadjibou Soumare shine shugaban hukumar ta Uemoa.

Yace ''taimakaon da muke samu daga ƙungiyar Tarrayar Turai na taimaka mana mu samu kudaɗen gudanar da aiyyukan ci gaba Kaman na aikin gona har ma da ɗaukacin aiyyuka na ci gaba''. Ko da yake mun fuskanci yan matsloli wajen samun kudin aiyukan asusun na goma saboda matsalar kudi da wasu ƙasashen Turai ke fuskanta, amma ni da shugaban Ecowas mun tinkari ƙungiyar tarrayar Turai, kuma sun nuna ƙarimci abinda ya sanya mu gudanar da wannan taro domin cimma yarjejeniyar aiwatar da aiyyukan bai daya.

Shirin samar da takardar kuɗin bai ɗaya tare da taimakon ƙungiyar Tarrayar Turai

Yunƙurin da ƙasashen ƙungiyar na Ecowas ke yin a samun kai wa ga samar da takardar kudi ta bai ɗaya dam asana harkokin tattalin arziki suka bayyana zata yi tasiri sosai wajen bunkasa tattalin arzikin yankin abinda ya sanya tambayar shugaban na kungiyar Ecowas Mr Kadre Desire ko me suka cimawa a game da wannan batu?

EU Gipfel Fahnen. Detailaufnahme von Flaggen europäischer Mitgliedsstaaten am Eingang des EU-Ratsgebäudes, Rue de la Loi, Brüssel. Ganz rechts an den Rand gedrängt Großbritannien. Aufgenommen 23.11.2012, Foto: Bernd Riegert, DW
Hoto: DW

Yace ''ka gani muna aiki tukuru domin mu tabbatar da mun cimma haɗewar takardar kudin ta zama bai ɗaya a tsakanin ƙasashen daf a cikin hukumar Umeoa suke ba, ta yadda za'a samu manufofin kuɗi na bai daya''. Ta haka zamu samu haɗewar takardun kudin su zama na bai ɗaya nan da shekara ta 2020 sanan mu samu takardar kudi ta bai daya a yankin mu.

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto