1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta kaddamar da shirin tallafa wa Afirka

Gazali Abdou Tasawa
January 19, 2017

Ministan ma'aikatar raya kasashe ta Jamus Gerd Müller ya kaddamar da sabon tsarin nan na tallafa wa kasashen Afirka da ake kira da "Marshall Plan", da nufin karfafa dangantakar Jamus din da kasashen nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/2W2sI
An kaddamar da shirin Jamus na tallafa wa kasashen Afirka mai taken "Marshall Plan"
An kaddamar da shirin Jamus na tallafa wa kasashen Afirka mai taken "Marshall Plan"Hoto: picture-alliance/dpa

Shirin wanda dama aka jima ana jiran fara aiwatar da shi na da burin kawar da duk wasu ababe da ke kawo tarnaki ga huldar cinikayya da saka jari a tsakanin Jamus da kasshen na Afirka. Da yake gabatar da sabon shirin nasa na "Marshall Plan" ga Afirka, ministan ma'aikatar raya kasashe ta Jamus, Gerd Müller ya bayyana cewa matakin yaki da talauci a nahiyar Afirka mataki ne da ko baya ga kasancewa na ya kamata, ya zamo mai muhimmanci sosai har ga kasashe masu karfin tattalin arziki kamar irin su Jamus din yana mai cewa:

"Ya zamo dole ga Jamus dama nahiyar Turai baki daya su ceci rayukan 'yan Afirka ta hanyar rage kaifin matsalar sauyin yanayi da samar da kyakkyawar makoma ga matasa idan dai har suna son magance matsalar kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira daga Afirka zuwa kasshensu."

Ministan ma'aikatar raya kasashe ta Jamus Gerd Müller
Ministan ma'aikatar raya kasashe ta Jamus Gerd MüllerHoto: picture-alliance/Sebastian Gol

Kundin sabon shirin na tallafawa Afirka mai kunshe da shafuka 33 ya tanadi sabon babi na hulda tsakanin kasashen Turai da na Afirka a fannoni kamar na ilimi da kasuwanci da kuma makamashi. Kazalika shirin ya tanadi saukakawa kasashen Afirka wajen fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin ketare da kawo karshen mu'amala da haramtattun kudade da ake sacewa daga Afirka domin boye su a ketare, dama kuma ajiyar kudaden da wasu 'yan Afirka ke yi a kasashen Turai da nufin kin biyan haraji a kasashensu. Bugu da kari sabon tsarin huldar da Afirka ya bukaci gudunmawar shugabannin Afirka a fannin yaki da cin hanci ta hanyar gudanar da shugabanci na gari da kuma kyautata rayuwar mata. Ofishin ministan raya kasashen na Jamus ya sha alwashin zuba kashi 20 daga cikin dari na kudaden aiwatar da sabon tsarin huldar dangantakar a kasashen Afirka da suka yi kokari wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka kamata kamar dagewa wajen samar da kudaden shiga na cikin gida ta hanyar haraji.

A hannu daya kuma kundin sabon babin huldar kasar ta Jamus da Afirka ya dauki matakai na ganin kamfanoni masu zaman kansu sun taka muhimmiyar rawa fiye da a baya wajen bunkasa tattalin arzikin Afirka ta hanyar taimaka musu da bashin kudade. Yanzu haka dai daga cikin kamfanoni dubu 400 da Jamus ta mallaka dubu daya ne kawai ke nahiyar Afirka sakamakon matsaloli na cin hanci da na rigingimun siyasa da makamantansu, a cewar Christoph Kannengießer babban darktan kungiyar Afrika Verein ta wasu kamfanonin Jamus 600 masu hulda da Afirka.