1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin ko ta kwana na Amurka da ƙawayenta

April 11, 2013

Amurka da Japan da Koriya ta Kudu na ci gaba da ɗaura damarar tinkarar barazanar da Koriya ta Arewa ke yi na harba musu makamai musu linzami kan nan da 15 ga watan Afirilu.

https://p.dw.com/p/18DzP
Hoto: picture-alliance/dpa

Amurka da Japan da Koriya ta kudu na cikin shirin ko ta kwana sakamakon barazanar da koriya ta Arewa ke yi na harba makami mai linzami akan abokan gabarta tare kuma da yin wani sabon gwajin makaman nukiliya. Jami'an hukumar leƙen asiri na Koriya ta Kudu sun ce ba mamaki Koriya ta Arewa ta harba makaman a ranar  15 ga wata na Afirilu, wace ta yi daidai da ranar  haifuwar  jagoran da ya kafa Tarrayar ta 'yan gurguzu wato  Kim Il Sung wanda ya mutu a shekarun 1994.

Ministan harkokin waje na Koriya ta kudun Yun Byung Se wanda ya yi  magana a gaban 'yan majalisun dokoki ya yi gargadin cewar gwaje gwaje na Koriya ta Arewan na iya faruwa a kowane lokaci inda ya ce "na tattaunawa da sakataran harkokin wajen Amurka akan wannan al'amari da muke bi sau da kafa".

Mawallafi: Abdourahmane Hassane
Edita: Mouhamadou Awal