1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin mika mulki ga sabuwar gwamanti a Najeriya

Ubale Musa/LMJMay 8, 2015

Ana samun takun saka tsakanin kwamitin mika mulki ga sabuwar zababbiyar gwamnati da kuma na karbar mulkin a Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1FN5g
Shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari da mai barin gado Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari da mai barin gado Goodluck JonathanHoto: U. Ekpei/AFP/Getty Images / AP Photo

Tuni dai aka kai ga kafa kwamitocin tare da tabbatar da samar musu ofisoshin yin aiki tsakanin jam'iyyar APC mai shirin karbar mulki da kuma 'yar uwarta ta PDP da ke shiri na adabo. To sai dai kuma a zahiri an shafe tsawon kusan makwanni biyu ana kwan-gaba-kwan-baya tsakanin APC da ke fadin babu gaskiya a zuciyar PDP na shirin mika mulkin da kuma 'ya'yan PDP da ke fadin APC ba ta shirin karbar mulkin sai surutu a baka. Tun a ranar 28 ga watan Afirilun da ya gabata ne dai aka tsara bangarorin biyu za su fara zama da nufin tabbatar da karbar mulkin a cikin sauki, kafin daga baya a daga zuwa hudu ga watan Mayun da muke ciki sannan kuma ka sake mayar da zaman zuwa 14 ga watan na Mayu. Ya zuwa yammacin Jumma'a takwas ga wannan wata na Mayu da muke ciki dai majiyoyi sun ce an sake dage zaman fara karbar bayanan mulkin zuwa 21 ga watan na Mayu.

Shugaba mai barin gado da mai jiran gado a Najeriya
Shugaba mai barin gado da mai jiran gado a NajeriyaHoto: DW/Ubale Musa

Mako guda kafin mika mulki

Sake dage zaman kwamitin zuwa 21 ga watan na Mayu da muke ciki dai na nuni da cewa kwamitin zai zauna ne mako guda rak gabanin wa'adin gwamnatin PDP a Abuja. Abun kuma da har ila yau ya tada hankula cikin APC da ke fadin an saba ka'ida kuma ana kokari na boye da dama daga cikin gyambon mulkin kasar ta Najeriya mai wari a fadar Sanata Lawalli Shu'aibu da ke zaman mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa. Tabargaza da dukiyar al'umma ko kuma kokari na tada hankali dai, da kyar da gumin goshi ne aka kai ga kwantar da jijiyoyi na wuya a tsakanin jam'iyyun da suka kai ga yakin neman zabe mai zafi suka kuma kare tare da bai wa marada kunya bisa sakamakon zaben.

Zargi a tsakanin PDP da APC

APC dai na kallon kokari na jan kafar a matsayin wani yunkuri na kautar da idanun jami'ai na gwamnatin da ke shirin hawa gadon ga yiwuwar gano tabargazar da ke kasa a ma'aikatu da hukumomi na gwamnati, karatun kuma da a tunanin gwamnatin da ke shirin barin gadon babu kanshi na gaskiya a cikinsa, a cewar Farfesa Rufa'i Alkali da ke zaman mashawarci na siyasa ga gwamnatin da ke shirin shudewa nan da ranar 29 ga wannan wata na Mayu da muke ciki. Abun jira a gani dai na zaman iya hada kan bangarorin biyu da nufin kai wa ga amintaccen tsarin da ake iya dora kasar domin ci gaba da kyautata rayuwar al'ummarta.

Babban ofishin jam'iyyar PDP na kasa da ke Abuja.
Babban ofishin jam'iyyar PDP na kasa da ke Abuja.Hoto: DW/U.Haussa