1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin samar da zaman lafiya a Ukraine

June 18, 2014

Shugaba Petro Poroschenko na Ukraine ya bayyana cewar dakarunsa za su tsagaita bude wuta nan ba da jimawa ba a gabashin kasar domin a yi sulhu da 'yan aware.

https://p.dw.com/p/1CLBH
Ukraine Präsident Petro Poroschenko 18.06.2014
Hoto: Reuters

Sanarwar da shugaba Poroschenko ya yi matakin farko ne na shirin samar da zaman lafiya da gwamnatin Ukraine ke shirin aiwatar a gabashin kasar Ukraine. Bisa ga wannan tsari dai masu neman ballewa za su iya mika makamansu domin a yafe musu laifukan da ake zarginsu da aikawata. Sannan kuma za su iya barin kasar ba tare da an yi musu bita da kulli ba. Sai dai shirin yafiyar na bukatar samun goyon bayan galibin bangarorin Ukraine da ke gaba da juna kafin a aiwatar da shi.

Tuni dai shugaba Poroschenko ya bayyana wa takwaran aikinsa na Rasha wannan matsayi nasa a lokacin da suka tattauna ta wayar tarho, dangane da kashe wasu 'yan jaridar rasha biyu da aka yi a fagen yaki a Ukraine. Ita dai kasar ta Rasha ta na nema a kafan kwamotin bincike mai zaman kansa domin gano musababbin mutuwar 'yan jaridan biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu