Shirin zaben shugaban kasa a Senegal

Al'ummar kasar Senegal na shirin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa a ranar Lahadi, a zaben da ba kamar yadda aka saba ba, shugaba mai ci Macky Sall ba ya fuskantar adawa mai yawa.

Macky Sall dai na ikirarin cewa yana da yakinin lashe zaben a zagaye na farko. Sall dai na shugabanci a kasar da malaman addinin ke da tasiri wajen zabar shugaba tun daga shekara ta 2012, inda a yaanzu zai fafata da 'yan takara uku kacal a zaben na ranar Lahadi 24 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki. Ana dai yi wa kasar ta Snegal kaallon abin koyi wajen zaman lafiya da fahimtar juna a nahiyar Afirka baki daya.  

Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka