1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye shiryen zaɓe a Nigeria

May 30, 2006
https://p.dw.com/p/Buw6

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta a Nigeria ta ce za ta kyale masu sa ido na ƙasa da ƙasa tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su na cikin gida, lura da yadda zaá gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana majalisun dokoki a Nigeria a watan Aprilu na shekara mai zuwa. Shugaban hukumar zaben Maurice Iwu yace zaá kyale jamián masu sa ido ne idan sun amince sun kuma martaba dokokin zaɓe na Nigeria ba tare da katsalandan ba. A ranakun 7 da kuma 28 ga watan Aprilu na shekara mai zuwa ne alúmar Nigeria za su kaɗa kuriá a zaben shugaban ƙasa dana gwamnoni da kuma na yan majalisun dokoki. Shugaban hukumar zaben ya ƙara da cewa wajibi ne masu sa idon na ƙasa da ƙasa su cika sharuda da ƙaídojin majalisar ɗinkin duniya na lura da harkokin zaɓe. Maurice Iwu yace a halin da ake ciki hukumar sa ta kamalla kashi 70 cikin dari na shirye shiryen zaɓen gwamnoni a ɗaukacin jihohi 36 na tarayyar Nigeriar mai yawan alúma miliyan 130. Tuni jamíyu 36 suka yi rajistar sunayen su da hukumar zaɓen inda ake sa ran zaɓar wanda zai gaji shugaba Olusegun Obasanjo. Zaben shekara ta 2007 shi ne zai kasance zabe na uku na mulkin dimokradiya a Nigeria tun bayan da ƙasar ta koma mulkin farar hula a shekara 1999.