1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tshisekedi ya lashe zaben Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango

Binta Aliyu Zurmi
December 31, 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango CENI ta ayyana Shugaba Félix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 20 ga watan Disamba.

https://p.dw.com/p/4akir
Felix Tshisekedi
Hoto: Boniface Muthoni/SOPA Images/ZUMA/picture alliance

Hukumar CENI ta ce Tshisekedi ya samu sama da kashi 73 cikin 100 na kuri'un da aka jefa a zaben da 'yan takara 20 suka fafata.

Moïse Katumbi Chapwe da Martin Fayulu wadanda su ne wadanda suka zo na biyu da na uku sun zargi CENI goyon bayan magudin zabe.

Tuni jam'iyyun adawa suka yi fatali da wannan sakamakon da ya baiwa Shugaba Tshisekedi damar yin wa'adi na biyu na tsawon shekaru biyar, kuma sun yi kira ga al'umma da su fito zanga zangar kin amincewa da matakin hukumar Ceni.

kasar ta Kwango dai da ke  tsakiyar Afirka mai arzikin albarkatun kasa na fama da matsaloli na tsaro da barazana daga 'yan tawayen M23.