1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da mutuwar Magufuli

Zainab Mohammed Abubakar
March 17, 2021

Tanzaniya ta tabbatar da mutuwar Shugaba John Magufuli mai shekaru 61 da haihuwa da ake wa lakabi "bulldozer", bayan makonni biyu na rashin ganinsa a bainar jama'a.

https://p.dw.com/p/3qmfT
  Shugaba John Pombe Magufuli
Shugaba John Pombe Magufuli Hoto: Tanzania Presidential Press Service

 Za a tuna shi a matsayin mutumin da yayi wa annobar COVID 19 rikon sakayyar kashi a Tanzaniya.

Tun bayan barkewar annobar corona a watan Maris a shekara ta 2020, Magufuli ya sha yin watsi dangane da kaifin wannan cuta balle illarta. A wani lokaci a baya, ya sha mayar da na'urorin gwajin coroina abun wasa, inda ya ce an tabbatar da cutar a jikin akuya da gwanda bayan gwajin samfurinsu.

Ya yi gargadin cewar, irin wannan sakamakon na nunar da cewar gwajin nuna cewar mutum ya kamu da cutar na iya zama karya. Jim kadan bayannan ne Tanzaniya ta tsayar da ba da bayanai kan yawan mutanen da corona ta kashe. Bayanan kartshe da ta bayar dai a watan Mayun bara ne. A lokacin an tabbatar da cewar mutane 509 sun kamu da COVID kana 29 sun rasa rayukansu.

A yayin da kasashen Kenya da Yuganda  makwabtaka ke aiwatar da dokar kulle da hana fita domin dakile yaduwar corona, shugaba Magufuli ya yi sanarwar ban mamaki na cewa, kofofin Tanzaniya na bude domin kasuwanci, kasancewar cutar bata da wani barazana. 

Ya ce" Mu 'yan Tanzaniya bamu kulle kanmu ba, kuma bana zaton sanar da koda rana daya ce na sanya dokar kulle, saboda ubangijin na nan, kuma zai cigaba da karemu. Sai dai zamu cigaba da daukar matakai na kariya da suka hadar sirace. Ka yi sirace, kana ka roki Allah, tare da cigaba da harkokinka na yau da kullum, ka ci abinci saboda ka karfafa garkuwar jikinka daga annobar corona".

An fara zaman makoki na Magufuli
An fara zaman makoki na MagufuliHoto: Said Khamis/DW

To sai dai tun bayan mutuwar mataimakin shugaban tsibirin Zanzibar Seif Sharaf Hamad daga cutar corona a watan Febrairu ne dai, Magufuli da mafi yawa daga Tanzaniyawan suka fara yin amana da hadarin kamuwa da kwayoyin cutar mai yaduwa. Daga bisani ma'aikatar lafiyar kasar ta gabatar- da sanarwar da ke rokon jama'a da su dauki matakan kariya.

A ranar 29 ga watan Oktoban shekara ta 1959 aka haifi Magufuli, kana ya samu digirinsa na biyu da na uku a shekarun 1994 da 2009 a jami'ar Dar el Salaam. Bayan koyarwa na gajeren lokaci a makarantar sakandare da Sengerema, da aiki kamfanin magunguna, Magufuli ya shiga siyasa a karkashin tutar jam'iyyar CCM.

An zabe shi zuwa majalisar wakilai a shekara ta 1995, kana daga bisani aka nada shi mataimakin ministan ayyuka. A shekara ta 2010 ya fara zama sananne bayan da aka bashi ministan sufuri da ayyuka a karo na biyu. Yanayin shugabancinsa mai tsanantawa da yaki da rashawa a ma'aikatar kula da gyaran hanyar, ya janwo masa kauna a tsakanin al'umma.

Ya samu farin jini tsakanin al'ummarsa da ma nahiyar Afirka baki daya, kan yaki da rashawa da yake yi a cewar masanin kimiyyar siyasa Martin Adati 

"Magufuli ya zo da akidar yaki da rashawa da karfafa talakawa. Mutanen da ke cin gajiyar rashawa da sauran abubuwa marasa kyau ne basa murna da shi".

A shekara ta 2015 ya yi takarar kujerar shugaban kasa inda ya lashe da kaso 58 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada, tare da kada abokin takararsa na jam'iyyar adawa ta Chadema Erdward Lowassa. Ya sake lashe zabe a 2020, bisa ga sakamakon da abokin adawarsa Tundu Lissu ya ayyana mai cike da magudi.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin jama'a na sukarsa da take hakkin al'umma d suka hadar da yancin tofa albarkacin baki da na 'yan jarida.

Shi ma madugun adawa da ke gudun hijira Tundu  Lissu ya ce, duk da nasarar da Magufuli ya samu, mulkinsa nada salon kama karya.

An fara zaman makoki na Magufuli
An fara zaman makoki na MagafuliHoto: Said Khamis/DW

"Ko shakka babu ya cimma duk wadannan nasarori, sai hakan bai bashi damar gudanar da mulkin kama karya ba, musamman irin dokokin da ya kakaba a kasar".

Shugaba Magufuli fitaccen mutum ne a Tanzaniya. Matakansa na rage barnatar da dukiyar kasa ya janyo mishi daukaka tsakanin al'ummarsa.