1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Robert Mugabe wird 90

February 21, 2014

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe na bikin cika shekaru 90 da haihuwa, wanda a kasashen Yammacin Duniya ake kallo a matsayin dan kama-karya. Amma a kasashen Afirka mutane masu yawa na masa kallon gwarzo.

https://p.dw.com/p/1BDRN
Hoto: Reuters

Robert Mugabe yana mulkin kasar ta Zimbabwe tun shekarar 1980 lokacin da kasar ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, kimanin shekaru 34 da suka gabata. Zai yi wuya Mugabe ya samu fatan alheri daga kasashen Yammaci bisa bikin cika shekaru 90 da haihuwa, saboda takun saka da ake samu tsakanin bangarorin kan salon mulkin da yake gudanarwa.

Wani babban abun tambaya shi ne, Robert Mugabe dan kama karya ne. Baffour Ankomah babban edita na mujallar New Afirka da ake wallakafawa a birnin London na kasar Birtaniya yana cikin wadanda suka san shugaban:

"Idan kana karanta jaridun kasashen Yammaci, za ka yi tunanin Robert Mugabe yana cin mutane. Amma idan da gamu da shi ido da ido, mutum ne na daban, za ka samu sabbin abubuwa, lokacin da kuka zauna kuka tattauna tare da shi."

A cikin shekara ta 2004 wannan mujalla ta nemi a gabatar mata da sunayen 'yan Afirka fitattu guda 100, kuma sunan Robert Mugabe ya zo na uku, bayan sunayen Nelson Mandela tsohon Shugaban Afirka ta Kudu da Kwame Nkrumah Shugaban Ghana na farko.

Shugaba Robert Mugabe da Sarauniyar Ingila Elizabeth cikin shekarar 1994
Hoto: picture-alliance/photoshot

Lamarin ya sauya, cikin shekaru 1980 zuwa 1990 Robert Mugabe mutum ne da ake girmamawa a kasashen Yammacin Duniya, bayan gwagwarmayar da ya jagoranta ta kwato 'yancin kan kasar Zimbabwe, Sarauniyar Ingila Elizabeth ta ba shi lamba yambo da digirin girmamawa.

Sunan Mugabe ya fara baci lokacin da tsageru suka mamaye gonakin Turawa da amincewar shugaban. Lamarin bai tsaya ga Turawa ba. A shekara ta 2005 gwamnati ta saka matsin lamba wa mutanen da suke zama a unguwannin marasa galihu da ke Harare babban birnin kasar da sauran manyan birane. An lalata fiye da gidaje 50,000 sannan an kama mutane 30,000, yayin da wasu kimanin milyan guda suka rasa matsuguni.

Andrea Jeska 'yar jarida kuma marubuciya tana cikin wadanda suka fito da abun da ke faruwa a kasar ta Zimbabwe:

"Zan iya tunawa, lokacin da na tambayi Joaqium Chissano tsohon Shugaban Mozambique, wanda yake bin tafarkin demokaradiyya, kan yadda yake hulda ta kut-da-kut da Robert Mugabe, wanda ya saba wa tafarkin demokaradiyya, abun ya fusata shi, amma ya amsa da cewa yaya zai kyale abokinsa lokacin da yake cikin mawuyacin hali."

Masu suka na ganin cewa Shugaba Mugabe ya dauki mataki kan marasa galihun saboda suna goyon bayan 'yan adawa. Kamen 'yan adawa da shugabannin kungiyoyin ya janyo tir daga kasashen Yammacin Duniya.

Amma duk da wannan kaurin suna na Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe akwai masu ganin yana cikin gwarzayen Afirka. Baffour Ankomah ya bayyana cewa:

Robert Mugabe
Hoto: Getty Images/Afp/Alexander Joe

"Abun da ya yi cikin shekaru 20 da suka gabata, shi ne mayar da gonaki hannun asalin wadanda suka mallaka, mutanen da aka yi wa fashi tun farko, wannan shi ya janyo wa Mugabe farin jini a Afirka, musamman kudancin Afirka, a Namibiya da sauran yankin."

Duk da halin da ake ciki, manufofin Shugaba Robert Mugabe na kasar ta Zimbabwe za su ci gaba da abubuwa da ke burge masu goyon bayan salon mulkin shugaban.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar