1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump na fuskantar guguwar siyasa a Amirka

Salissou Boukari
May 11, 2017

Tun bayan da ya tsige babban Darectan hukumar leken asirin kasar ta Amirka ta FBI James Comey, Shugaba Donald Trump na fuskantar wata guguwa ta siyasa kan dalillan tsige Comey a wannan lokaci.

https://p.dw.com/p/2cm1N
USA Donald Trump und James Comey
Shugaban Amirka Donald Trump tare da James Comey shugaban hukumar FBI da ya koraHoto: Getty Images/A. Harrer

A wannan Alhamis din ce (11.05.2017) dai Darectan riko na hukumar ta FBI Andrew McCabe, zai fuskanci babban kwamitin nan na 'yan majalisar ta Amirka masu kula da fannin tattara bayannai domin bada ba'asi, kuma daya daga cikin kwamitocin da ke bincike kan tuhumar da ake yi wa kasar Rasha da yin kutse kan zaben na Amirka. Hakan ta sanya wasu 'yan majalisa guda biyu daga bangarorin biyu, ke aza ayar tambaya kan dalillan cire Darectan na hukumar FBI a daidai wannan lokaci, kuma tuni 'yan adawa suka soma zargin Shugaba Trump da neman yin kafar ungulu kan binciken da ka iya shafa masa kashin kaji. Sai dai kuma Shugaba Trump din ya ce matakin ba shi da wata alaka da binciken da ake yi.