1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Zelensky da Xi Jinping

Binta Aliyu Zurmi
April 27, 2023

Shugaban Volodmyr Zelensky na kasar Ukraine a karon farko tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a kasar sa ya yi wata tattaunawa mai tsawo ta wayar tarho da shugaba Xi Jingping na kasar China.

https://p.dw.com/p/4QbwJ
Ukraine Präsident Wolodymyr Selenskyj
Hoto: president.gov.ua

Kyiv wacce ta kwashe watanni tana neman tattaunawa da China don yin amfani da alakarsu da Rasha na ganin ta taimaka kawo karshen yakin da suka kwashe sama da shekara suna gwabzawa.

Zelensky ya bayyana tattaunawar ta wayar tarho mai tsayi da kuma ma'ana, kazalika ya kara da cewar yana fata ta yi sanadin kawo karshen wannan fada.

To duk wannan dai na zuwa ne bayan da Rashar ke kara zafafafa hare-hare a yankin garin Bakhmut da ke gabashin kasar Ukraine wanda rahotanni suka tabbatar an harba rokoki sama da sau 150 a tsukin kwana guda, a yunkuurin karbe iko da yankin gabaki daya.


China ta yi alkawarin aike wa da wakilai na muusamman izuwa birnin Kyiv.