1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Zuma ya tsallake rijiya da baya

August 8, 2017

Yunkurin tsige shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu da 'yan majalisar dokoki suka yi ya ci tura, Zuma dai ya sami goyon bayan 'yan jam'iyyarsa ta ANC da ke da rinjaye a majalisar

https://p.dw.com/p/2httH
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Yunkurin tsige shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu da 'yan majalisar dokoki suka yi ya ci tura, Zuma dai ya sami goyon bayan 'yan jam'iyyarsa ta ANC da ke da rinjaye a majalisar, wannan ya kasance karo na bakwai da ake kada kuri'ar yanke kauna ga shugaban ba tare da an sami nasarar ba.

Zarge zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa shugaban da kuma halin tabarbarewar tattalin arzikin kasar na daga cikin dalilan neman Zuma ya ajiye mukaminsa. Yanzu dai zai ci gaba da jan ragamar mulki har zuwa cikar wa'adin mulkinsa a shekarar 2019.

An sami kuri'u dari daya da saba'in da bakwai sabanin dari biyu da daya da ake bukata kafin a yi nasarar tsige shugaban.