1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Hassane Rouhani a Faransa

Kmaluddeen SaniJanuary 28, 2016

A ranar alhamis din nan ce shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya sudu da shugaban kasar Faransa Francois Hollande a ziyarar daya kai kasar domin tattaunawa a bangarorin kara habaka dangantaka a tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/1HlVX
Rohanis Besuch in Frankreich
Hoto: Reuters

Dukkanin shugabanin biyu dai zasu tattauna ne akan irin rawar da zasu taka ne a musamman a kasashen Syriya da Yemen gami sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi a tsakanin su.

Kazalika Shugaba Hassane Rouhani da Francois Hollande za kuma su rattaba hanu akan wasu yarjeniyo 20 domin kara habaka harkokin kasuwanci da huddar diplomasiya a tsakanin su.

Ayayin jawabin sa a gaban kungiyar 'yan kasauwar Faransa Hassane Rouhani yace :Mun hallara ne a nan domin tattauna batun harkokin kasuwanci gami da kara karfafa dangantaka ta Faransa tare da yin aiki da Faransan kan makamashi hade da jajircewa da a bangaren siyasar Iraniyawa a yau.

Kazalika Francois Hollade ya jinjinawa kasar Iran abisa yarjeniyoyin da suka rattabawa hannu gami yunkurin ta na sake bude wani sabon babi da kasashen duniya.