1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Nijar na neman shawo kan matsalar lantarki

April 8, 2013

A daidai lokacin da Jamus ke daukar bakwancin taron kasa da kasa kan makamashi, Jamhuriyar Nijar na fama da karancin wutar lantarki. Sai dai hukumomi sun dukufa wajen wadata kasar da karin makamashi.

https://p.dw.com/p/18BpO
Hoto: AP


Hukumar kididdiga ta Jamhuriyar Nijar ta nunar da cewa a shekara ta 2012 kasar ta yi amfani da wutar lantarki da ya kai yawan Megawatts 550. Wannan na nufin cewa kashi 8% na fadin kasar ne ke cin gajiyar wannan makamashi a garuruwa kimanin 300 na kasar. A halin yanzu ma dai akwai makeken gibi tsakanin kauyuka da kauyuka; inda kashi 44% na mazauna birane ke samun lantarki yayin da kasa da 2,5% na yankunan karkara ke amfani da wutar lantarki. Kashi 64% na wutar lantakin da ake sha a Jamhuriyar Nijar na fitowa ne daga makobciyarta Tarayyar Najeriya.

Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Majalisa ta amince da shirin samar da karin wutar lantarki.Hoto: DW

Sai dai akasarin garuruwan da su ke amfani da lantarkin a Nijar na fama da tsikewarta a a lokutta da dama musammana lokutan zafi wato kaka. Masana'antu ciki kuwa har da na birnin Yamai na amfani da janareto bayan katsewar wutar lantarki domin samun makamashin da suke bukata. Wannan matsala na kawo cikas a harakokin yau da kullan na al'uma da ma masana'antu. Saboda haka ne suke yawaita yin korafi game da wannan matsala.

Matakan cike gibin wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar
A 'yan shekaru nan gwamnatin kasar Nijar ta dukufa wajen samar da hanyoyin shawo kan wanann matsala ta karancin wutar lantarki. A makon da ya gabata(04.04.2013) gwamnati ta gudanar da bikin dora tubalin farko na gina wata sabuwar cibiyar lantarki da za ta samar da karin Megawatts 100. Ministan makamashi da fetur na Nijar Fumakoy Gado ya ce matakai da dama gwamnatinsu ta dauka domin magance karancin wutar lantarki a Jamhuiriyar Nijar.Fadar mulki ta Yamai ta kuma dukufa wajen samar da makamashin lantarki ta hanyar hasken rana a inda tuni kanfanin man fetur da kasar ta mallaka ya lamshe kashi 10% na makamashin da kasar ke amfani da shi.

Niger portioniertes Benzin in Maradi
Matatar fetur na daga cikin kanfanonin da ke bukatar karin makamashiHoto: picture-alliance/ZB

Rahotanni cikin sauti na kasa

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe