1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Siri Lanka yana ziyara a ƙasar Indiya

Suleiman BabayoFebruary 16, 2015

Sabon Shugaban ƙasar Sri Lanka Maithripala Sirisena ya fara ziyarar aiki ta farko a kasashen ƙetere

https://p.dw.com/p/1EcaH
Sri Lanka Präsidentschaftswahlen Maithripala Sirisena 9.1.2015
Hoto: AFP/Getty Images/S. Kodikara

Sabon Shugaban ƙasar Sri Lanka Maithripala Sirisena ya fara ziyarar aiki ta farko a ƙasashen ƙetere da ƙasar Indiya inda ya ƙulla yarjejeniyoyi da Firamnista Narendra Modi a fannin aikin gona, da nukiliya domin makamashi da wasu fannoni.

Indiya ta nuna damuwa lokacin mulkin tsohon Shugaban ƙasar ta Sri Lanka Mahinda Rajapaksa wanda ya mayar da hankali kan ƙasar China, bayan kawo ƙarshen yaƙin basassan shekaru 26 a shekara ta 2009 kusan shekaru shida da suka gabata, amma bisa wannan ziyara ta Shugaba Sirisena haka zai ƙarfafa ƙarfin danganka tsakanin biyu.