1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanni na son sabuwar makoma ga duniya

Yusuf BalaSeptember 25, 2015

Wannan dai na zuwa ne cikin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amirka da ke da burin samar da ci-gaba mai dorewa a kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/1GdLB
USA UN-Menschenrechtsrat in Ney York
Mahalarta taron Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/dpa/P. Foley

Shugabannin kasashen duniya a wannan Jumma'a a birnin New York na Amirka a taron kolinsu zai amince da shirin kakkabe bakin talauci da yaki da sauyin yanayi da ma wasu batutuwa da ke zama kalubale a tsakanin kasashen duniya, karkashin wani tsari da zai lakume makuden kudade cikin burin da suke da shi a tsawon shekaru 15 masu zuwa.

Wannan sabon shirin samar da sauyi na ci gaba, ana sa ran za a kashe tsakanin Dalar Amirka Tiriliyan uku da rabi zuwa tiriliyan 5 a kowace shekara har zuwa 2030.

Shugabannin da ake sa ran jawabansu a yayin taron kolin sun hada da Shugaba Barack Obama na Amirka da Xi Jinping na China da kuma shugabannin kasashen Masar da Iran da Indiya da Jamus da Birtaniya da kuma Faransa.