1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin G7 na taron koli a Italiya.

May 26, 2017

Taron kolin kasashen G7 zai yi kokarin dinke barakar da ta fito fili a tsakaninsu kan yaki da ta'addanci da cinikayya da kuma sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/2dak2
Italien G7 Außenministertreffen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/ANSA/R. Dalle Luche

Shugabannin kasashe bakwai masu cigaban masana'antu na duniya G7 sun hallara a birnin Sicily na kasar Italiya domin fara taron koli na yini biyu da kuma kokarin tabbatar da hadin kan su kan batutuwan yaki da ta'addanci da cinikayya da kuma sauyin yanayi.

Firaministar Birtaniya Theresa May za ta jagoranci tattaunawa kan yaki da ta'addaci inda ake sa ran za ta bukaci kasashen bakwai masu cigaban masana'antu su matsa lamba kan kamfanonin sadarwar Internet su cire dukkan wasu bayanai da suka shafi tsattsauran ra'ayi ko akida a shafukan Internet.

Taron na bana wanda ya sami halartar sabbin fuskoki da suka hada da Theresa May ta Birtaniya da Emmanuel Macron na Faransa da kuma Donald Trump na Amirka na zama zakaran gwajin dafi kan yadda ake kallon sabuwar gwamnatin Amirka za ta aiwatar da manufarta musamman akan sauyin yanayi da shugaba Trump ya yi alkawarin cire kasarsa daga yarjejeniyar rage hayakin masana'antu da aka cimma a taron muhalli na duniya a Paris.

Ana sa rai taron zai tattauna rikicin Siriya da Libya da kuma Koriyar ta Arewa.