1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siliman tafi da gidanka a Afrika ta Kudu

Abdu-raheem Hassan/ GATJuly 22, 2015

Wani matashi mai suna Calvin Phaala ne ya fito da fasahar domin bawa mutanen karkara da ba su da akwaitin talabijin damar kallon wasannin kwaikwayo a saukake.

https://p.dw.com/p/1G2a2
Lagos Photo Festival - Afrika zwischen Megacity und Dorfleben
Hoto: Lagos Photo Festival

Calvin Phaala wani matashi mai kimanin shekaru 24 da haihuwa wanda ya fito da wannan fasaha inda a kowane dare na Allah yake amfani da majigin nasa wanda yake haskawa a bisa wani kyalle da yake bugawa a jikin gini a madadin akwaitin talabijin. Ta hanyar wannan majigi ya ke bawa al'ummar kauyensu na Garinsa damar kallon wasanni kwaikwayo musamman irin na cikin gida. Kuma tarin jama'a ne ke taruruwa a kowane dare domin kashe kwarkwatar idanunsu.

Mandela Beerdigung Südafrika
Hoto: DW/D. Pelz

Kwalliya na biyan kudin sabuni a sana'ar

Wannan sana'a dai ta sa Calvin zama fitaccen gwarzo a fagen nishadantarwa a garin Siyabuswa, inda ya shafe watanni biyu ya na wannan sana'a kuma da alamu kwalliya na biyan kudin sabulu tunda akalla bai gaza samun sama da dala takwas a duk mako. Sai dai Calvin ya ce wannan sana'a tasa na fuskantar kalubale.

"Babban kalubale gareni dai shi ne masu satar fasaha, mutane na samun sabbin fina-finai, amma na jabu ne. Ni kuma ba zan iya nuna fina-finan jabu ga al'umma ba."

Al'umma na yabawa da fasahar Calvin

A wani kokari na neman bunkasa wannan sana'a tasa lokaci zuwa lokaci Calvin na bin gida gida wajen wayar wa al'ummar kai dangane da mahimmancin gidan kallon fina-finai ga zamantakewarsu ta duniya. Nombulelo Trudy Qwasho, daliba ce da ke bayyana gamsuwarta kan himmar da Calvin ke da ita wajen cimma burinsa.

Kongo Fußball WM 2010
Hoto: AP


"Babu gidajen kallo, ko wuraren da za'a kalli fina-finai, balle ma a ce irin wuraren debe kewa tare da abokan arziki."

Wannan aiki na fina-finai dai, ya bunkasa kasuwancin Calvin matuka. Kuma har ya soma tanadin wata sabuwar sana'ar ta saida abinci da mahaifiyarsa a duk lokacin da ake nuna fina-finan da ke basu damar samun wasu kudaden shiga.