Siriya: An zargi wakilin Majalisar Dinkin Duniya

'Yan adawa a Siriya sun yi Allah wadai da Staffan de Mistura wakilin Majalisar Dinkin Duniya bayan ya bukaci kawo karshen yan ta'addan dake yankin Idlib.

Da yake karin bayani Yehia Arid guda cikin wakilan 'yan adawa a tattaunawar sulhun da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta kan rikicin na Siriya ya zargi Mistura da ingiza gwamnatin kasar Siriya ta yi amfani da makami mai guba wajen kai hari yankin na Idlib.

Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka