Siriya: 'Yan gudun hijira na yin kome

Jami'an tsaron kasar Lebanon, sun sanar da cewa kimanin 'yan gudun hijira 1,000 daga Siriya sun koma gida.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya SANA, ya ruwaito cewa komawar 'yan gudun hijirar na zaman wani bangare na yunkurin gwamnatocin kasashen Siriyan da Lebanon na ganin an mayar da 'yan Siriyan da ke zaune a Lebanon din gida. Dubban 'Yan Siriya ne dai yakin kasar ya tilasta musu tserewa zuwa Lebanon din da sauran kasashe makwabta da ma nahiyar Turai. A cewar kamfanin dillancin labaran na Siriya SANA, wadanda suka koma sun fito ne daga gundumar Homs da biranen Damascus da Hama, da ke zaman yankunan da aka karbe daga hannun kungiyar 'yan ta'addan IS. 

Rahotanni masu dangantaka