1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasa da tsaro a Afirka sun dauki hankalin jaridu a Jamus

Mohammad Nasiru Awal MA
November 16, 2018

Galabar da mata ke samu a siyasar kasashen Afirka da ziyarar nazarin halin tsaro a Mali sun dauki hankalin jaridu a Jamus.

https://p.dw.com/p/38NqL
Äthiopien Ethiopian Women Lawyer Association
Wasu daga cikin mata masu mukamai a AfirkaHoto: DW/G. Tedla

Jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta buga labari kan yawan mata da ke samun manyan mukaman siyasa a Afirka ta ce siyasar Afirka na komawa hannun mata, koda yake samun shugabancin kasa ne babbar matsala a gare su.

Jaridar ta ce da yatsar hannu za a iya kirga yawan matan da suka taba rike mukamin shugaban kasa a nahiyar Afirka. A 'yan shekarun da suka gabata mata ba su da wakilci a majalisun dokokin wasu kasashen Afirka, amma yanzu an fara samun sauyi. A tsakiyar watan Oktoba Firaministan kasar Habasha ya gabatar da sabuwar majalisar ministocinsa, da mata suka cike rabin mukamai. Sannan kwanaki kalilan bayan haka aka zabi mace a karon farko shugabar kasar da ke yankin Kahon Afirka.

A Ruwanda shugaban kasar ya ce mata za su rike rabin mukamai a cikin gwamnatinsa. A watan Afrilu kasar Botswana ta nada Bogolo Kenewendo 'yar shekara 31 mukamin ministar ciniki, sannan a watan Satumba Kamissa Camara 'yar shekara 35 ta karbi mukamin ministar harkokin wajen Mali. Jaridar ta ce wannan dai ci gaba ne mai ma'ana ga mata a nahiyar ta Afirka, sai dai har yanzu akwai rashin daidaito na tattalin arziki da ilimi da karfin fada a ji tsakanin maza da mata a nahiyar.

Verteidigungsministerin von der Leyen in Mali
Ministar tsaron Jamus a wata ziyara a MaliHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi kan ziyarar da ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta kai kasar Mali a farkon mako. Jaridar ta fara ne da tambaya me sojojin Jamus kimanin 1000 da aka girke a Mali za su iya yi a wannan kasa mai cike da matsaloli, na rashin hukumomi na a zo a gani da rigingimun kabilanci da ta'addanci?

Jaridar ta ce za su iya ba da gudunmawa idan aka samu cikakken hadin kai da manya da masu karfin fada a ji a yankin musamman kasar Faransa. Jamus ta kwashe shekaru da yawa tana aikin raya kasa a Mali, amma yanzu sojojinta na ba wa takwarorinsu na Mali horo don karfafa musu gwiwa. Har yanzu masu kaifin kishin addini na ci gaba da zama babbar matsala a Mali musamman a arewacin kasar.

Mosambik - Einweihung der Maputo-Katembe-Brücke: größte Hängebrücke Afrikas
Hoto: DW/R. da Silva

 A nata bangaren jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta leka kasashen Kwango ne guda biyu tana mai cewa za a gina wata gada mai muhimmanci tsakanin biranen Brazzaville da Kinshasa. Jaridar ta ce biranen biyu su ne manyan birane mafi kusa da juna wanda kogin Kwango ya raba su, amma babu wata gada da ta ratsa kan kogin. A dole matafiya na amfani da jiragen ruwa don tsallake wannan kogi.

Amma yanzu bankin raya kasashen Afirka da wani kamfani mai zaman kansa daga Afirka ta Kudu sun samar da kudi dala miliyan 550 don gina gadar da za ta yi tsawon kimanin kilomita daya da rabi. Za a yi mata hanyoyin mota mai shiga da fita guda hudu da layin dogo daya da kuma wata hanya da mutae za su rika bi kanta suna tsallake kogin. Sai dai za a rika biyan kudin hanya wato Toll-Gate. Jaridar ta ce wannan aiki zai taimaka a kawar da abin da aka gada daga 'yan mulkin mallaka wadanda suka mayar da kogin layin iyaka tsakanin kasashen Kwango guda biyu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani