1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasa ta dauki wani salo a Habasha

Abdul-raheem Hassan
February 16, 2018

Matakin murabus daga aiki da Firaministan kasar Habasha ya yi na ci gaba da janyo martanin masu sharhi daga ciki da wajen kasar. Babban abin dai shi ne na matsaloli na siyasa dake jiran wanda zai gaje shi.

https://p.dw.com/p/2sp2A
Äthiopien kündigt Freilassung politischer Gefangenen an | Hailemariam Desalegn
Desalegn
​Hailemariam Desalegn, Firaministan Habasha mai murabusHoto: picture alliance/AA/E. Hamid

Ajiye aikin Firamistan Habasha a ranar Alhamis, ya sauya al'amuran siyasar kasar da ma nahiyar Afirka baki daya. Murabus din Hailemariam Desalegn ya biyo bayan bayan yajin aiki da jerin zanga-zangar neman sako karin wasu fursunonin siyasa da ke a tsare. Gwamnatin ta 'yantar da fursunoni sama da 6,000 daga watan Janairu ya zuwa yanzu, a wani mataki na dadada wa manyan kabilun kasar na Oromo da Amhara wadanda ke kokawa da rashin adalci. Firaministan ya ce ajiye aikinsa gudmmuwa ce ga warware sarkakiya da kasar ke ciki. 

Äthiopien Kaliti Gefängnis
Lokacin sakin fursunonin siyasar HabashaHoto: DW/Y. Gebregziabher

Murabus na Firamistan na zama babbar kalubale ga kasar ta Habasha, ganin yadda za a samu rarrabuwar kawuna a jam'iyyun da suka kafa gwamnatin hadaka. Kawo i yanzu babu tabbacin wanda zai gaji Desalegn a matsayin sabon Firamistan Habashar.

 

Kasar Habasha dai ta yi zarra ta fuskar tattalin arziki yankin, sannan ta yi nasara wajen cimma karfin kungiyoyin 'yan ta'adda. Sai dai a share guda akwai rikicin kabilanci da ke addabi kasar. Wannan ya sa Mantegaftot Sileshi na sashin Amharic a DW ke ganin matakin Firaminista ba shi da tasiri wajen warware matsalolin kasar.
 "Bana tuna wannan mataki zai taimaka wajen warware sarkakiyar siyasar da ke kasar Habsha. A gani na mafita ita ce tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa ba ma jam'iyyun da ke cikin gida ba kadai, amma har da wadanda ke waje, sai dai idan matakin ya samo asali daga uwar jam'iyya za a iya cewa canji ne babba a kasar Habasha"

A baya dai jami'an tsaron kasar sun kashe daruruwan mutane yayin hatsaniyar ta barke tsakanin manyan kabilun kasar na Oromiya da Amhara a shekarar 2015 da kuma ta 2016.