1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar makamashi a taƙaddmar Rasha da ƙasashen yamma kan Ukraine

March 11, 2014

Wasu ƙasashen Turan dake dogaro da iskar gas daga Rasha na hasashen wata ƙila su sauya wurin samun makamashin idan dai Rasha ba ta ba da kai bori ya hau dangane da Ukraine ba

https://p.dw.com/p/1BNbK
Kerry und Lawrow in Rom 06.03.2014
Jami'an diplomasiyyar Amirka da RashaHoto: Kevin Lamarque/AFP/Getty Images

Ƙasashen Ukraine da Jamus duk suna dogaro ne da ƙasar Rasha a harkar makamashin gas, ganin cewa yanzu sun shiga taƙaddama da Rasha, ƙasashen za su gwammace sayo gas din nasu daga kasar Amirka, domin mayarwa Rasha anniyarta bisa rikicin da ake yi da ita? Wannan dai shi ne ra'ayin gwamnan jihar Texas na ƙasar Amirka Rick Perry.

Tun a shekara ta 2005 ne ƙasar Amirka ta fara samar da makamashi ta hanyar amfani da sinadarai da ruwa domin fidda makamashin gas daga cikin duwatsu. A yanzu haka akwai tulin irin waɗannan makamashin da aka sarrafa da ruwa da sindarai, kuma farashinsu bai taka kara ya karya ba.

USA Ukraine Demos 06.03.2014 Washington
Har a Amirka an yi zanga-zangar nuna goyon baya ga UkraineHoto: Reuters

Waɗannnan dabarun ne ƙasar Amirka samarwa kanta makashin, haka zalika wasu yan siyasan Amirka na yin kiran a rika tura makamashin gas daga Amirka zuwa Ukrain da wasu kasashen Turai, ta yadda za su rage dogaro da kasar Rasha bisa samun makamashi.

A wata zaman da majalisar dattawan Amirka ta yi an tambayi ƙaramin sakataren harkokin wajen Amirka William Burn ko hakan gwamnatin Obama na shirin dage dokar takaita sayarda makashin gas da na mai zuwa ketare da ake amfani da ita yanzu, sai yace.

"Ana matuƙar duba matakai da yawa, ta waɗanne dabaru ne tsarin harkokin wajenmu zai yi tasiri bisa wannan taƙaddama da ake ciki?Kuma muna duba yiwuwar ɗaukar wannan matakin, domin ƙasashe kamarsu Rasha sun daɗe suna amfani da makamashin da suke da shi a matsayin matakin siyasar kare tsaron cikin gida"

Symbolbild Russland Ukraine Gaslieferung
Bututun gas daga Rasha zuwa UkraineHoto: picture-alliance/dpa

Ƙudurin mahukuntan Washington dangane da rikicin Ukraine

A zahiri mahukuntan Washinton na son shugaba Putin ya shiga halin ƙaƙa nika yi, kan batun dogaron da ƙasashen Turai ke yi da bisa samun mai da iskar gas daga Rasha, to amma a gefe guda ita kanta Amirka za ta ji jiki, idan tattalin arzikin Rsaha ya yi rauni, domin kuwa hakar mai zai ragu a Rasha, kuma hakan zai haddasa matsalarsa a duniya, to amma fa akwai Amirkawa masu yin bambaɗancin samun tsadar mai a cikin gida, amma suma su sayarda tsada a waje.

To sai dai a cewar Sanata Edward Markey, rikicin Ukraine bai kamata ya kasance abin da zai kawo matsala ga makomar harkar makamashin cikin gida ba.

"Wannan tatsuniya ce, ba za mu tura gas dinmu zuwa Ukraine ba, babu shugaban kasar Amirka da zai bada umarnin hakan, ba za mu iya yin gogayya da Rasha ba kan Ukraine, domin Rasha na da bututu har cikin Ukraine farashinsu ba za a hada da namu ba. Ya kamata majalisa ta sake tunani, za mu iya taimakawa China da latin Amirka da makashinmu, sannan mu dawo cikin gida muna danɗana kudarmu. Wanda ba zai tasiri ba rikicin Ukraine, yan kasarmu za su dawo daga baya suna tambaya, shin wane tunani ya kai shugabannin suka yi tsaula mana farashin makahsin da mu ke da shi"

Martanin al'ummomin Amirka

A cikin gwamnatin ta Amirka dai, ana ɗaukar waɗannan batutuwa da mahimmanci domin sanin abin da ka iya aukuwa. Idan ana son fara tura makamashin gas zuwa ketare, to dole sai an ingata ko kuma gina ƙarin sabbin tashoshin jiragen ruwa da za a hadawa kayayyakin ɗibar mai da jiragen ruwa, kuma yanzu irin waɗannan tashoshin biyar ake kan ginawa a Amirka wadanda kuma aiki ne mai bukatar makudan kudi, nan da shekaru biyu za a kammala tashoshi biyu daga ciki.

Russland Wladimir Putin Gazprom
Putin a wajen bututun iskar Gas na GazpromHoto: dapd

A Turai ma yanzu ne wasu kasashen suka fara gina tashoshin jiragen ruwa ne jigilar iskar gas, kamar a Poland da Hamburg a kasar Jamus. Don haka karamin sakataren harkokin wajen Amirka William Burne ya ce:

"Kasar na bukatar samar da matakan samun masakshi da kanta, misali ta gina jiragen ruwa masu dakon iskar gas"

Gwamnatin kasar ta Amirka dai yanzu ta shirya wata kwangilar biliyoyin daloli da kasar Ukraine, inda za a samawar Ukraine jiragen ruwa masu dakon iskar gas, ta hanyoyin samar da iskar gas da Amirka ke yin amfani da su yanzu wato amfani da sinadarai da ruwa domin fidda makashin gas daga cikin duwatsu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Pinaɗo Abdu Waba