1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar wasu kasashen Afirka su ja hankalin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala MA
October 12, 2018

A wannan makon wasu daga cikin jaridun Jamus sun yi sharhi ne kan siyasa da zabe ne da aka yi a wasu kasashen nahiyar Afirka. 

https://p.dw.com/p/36Ri2
Kamerun Präsidentschaftswahlen Unterstützer von Maurice Kamto
Wasu lokacin gangamin siyasa a KamaruHoto: Reuters/Z. Bensemra

Jaridar Neue Zürcher Zeitung  ta yi duba ne kan tsarin kada kuri'a da na'urar kwamfuta. Ta ce galibin zabuka a Afirka ba sa ma'anar da suke nufi. Ko da yake ana gudanar da yakin neman zaben a wurare da dama da jawabai a ko ina a cikin kasa tare da sauki irin na siyasa. To amma ainihin zaben kan kasance suna ne kawai, inda masu karfin iko da wadanda ke kan karagar mulki ke nuna karfin tasiri. 

Jaridar ta ce misali na irin wannan karfin tasiri shi ne Kamaru, inda a ranar Lahadin ta gabata jama'a suka kada kuri'a. Kasar ta yammacin Afirka da shugabanta Paul Biya mai shekaru 85 a yanzu wanda kuma ke neman tazarce ya shafe shekaru 36 yana mulki. Zaben da ake yi wa kallo a matsayin cikon al'ada, hatta ma dai 'yan adawa wadanda kansu bai hadu ba, sun san cewa ba su da wata dama ta darewa karagar mulki. Sai dai wani dan adawa Maurice Kamto ya ce motsi ya fi labewa, ya kuma dauki wannan kalubale na karawa da shugaban mai ci a wannan zabe. 

Kamerun Präsidentschaftswahlen l Maurice Kamto MRC
Maurice Kamto na jam'iyyar MRC a KamaruHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Kamto ba shi ne dan Afirka dan adawa na farko da ya ayyana samun nasara tun gabanin bayyana sakamakon zabe ba. Ko da a Zimbabuwe an sami bangarori biyu da kowannensu ya bayyana samun nasara. Haka ma a Mali da kuma Kenya inda Raila Odinga shi ma ya bayyana cewa shi ya yi nasarar lashe zaben kasar.

 

Wannan dai na nuna irin kalubale da kuma rashin nagarta na hukumomin zaben wajen tabbatar da gaskiya da adalci. A waje guda kuma kotuna da jami'an tsaro da kuma kafofin yada labarai rashin ingancin ci gaban fasaha wajen samun sahihan bayanai sun sanya ana iya murda sakamakon zabe cikin sauki. Jaridar ta ce kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ya bayyanar da wannan kalubale a kasashe da dama na Afirka.

A nata sharhin Jaridar die tageszeitung ta yi tsokaci ne kan takarar zaben neman kujerar shugabancin kasa a Najeriya.

Jaridar ta ce Oby Ezekwesili wadda ta yi shura da taken #BringBackOurGirls wajen fafutikar ceto 'yan mata 'yan makarantar sakandaren Chibok da 'yan Boko Haram suka sace a shekarar 2014, ta kudiri shiga takarar shugabancin kasar da za a gudanar a watan Fabrairun 2019 karkashin wata karamar jam'iyya Allied Congress Party of Nigeria. Sai dai kuma ko wane tasiri za ta yi, sakamakon zaben ne zai nuna.

Muna bukatar hada hannu da Afirka, inji jaridar Süddeutsche Zeitung.
Jaridar ta ambato ministan raya kasashe na Jamus, Gerd Müller, yana kira ga kungiyar Tarayyar Turai ta samar da ingantacciyar manufa ta raya kasa ga Afirka. Ya ce akwai bukatar manufa ta bai daya na kasashen Turai da zai kunshi samar da karin kudaden raya kasa. Kasafin kudin kungiyar Tarayyar Turai EU da zai gudana tsawon shekaru bakwai zuwa 2020 ya tanadi samar da karin euro biliyan shida ne kacal ga Afirka wanda ya yi kadan matuka a cewar ministan. To sai dai ya ce akwai bukatar gani a kasa maimakon yawan magana ta fatar baki. Ga Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Jamus hada hannu da Afirka bai kamata ya tsaya ga batun 'yan gudun hijira ba kadai. Ya kamata likafar ta wuce nan.

Der südafrikanische Präsident Cyril Ramaphosa (links) schüttelt mit dem neu gewählten Finanzminister Tito Mboweni in Kapstadt, Südafrika, die Hand
Hoto: picture alliance/AP Photo

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tabo dambawar da ta ritsa da ministan kudin Afirka ta Kudu. Jaridar ta ce babu wanda ya yi tsammani ko ya hango cewa kwatsam Tito Mboweni zai zama ministan kudin Afirka ta kudu. Nadinsa ya biyo bayan murabus din tsohon minista Nhlanhla Nene sakamakon badakalar dangantaka da Iyalan Gupta da suka yi kaurin suna bisa zargin juya akalar gwamnati a zamanin tsohon shugaban kasa Jacob Zuma.