1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Chadi da Nijar sun kwato Damasak

Ahmed SalisuMarch 9, 2015

Sojin kasar Chadi da na Jamhuriyar Nijar sun kwato garin nan na Damasak da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar bayan da suka tafka fada 'yan kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1Enfu
Soldaten aus dem Tschad Archiv 2014
Hoto: AFP/Getty Images/M. Medina

Rahotanni daga Najeriya na cewar sojojin Chadi da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar sun samu nasar karbe iko da garin nan na Damasak da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram, suka karbe iko da shi a watan Nuwamban da ya gabata.

Gabannin karbe iko da garin wanda ke kan iyakar Najeriya da Nijar, sojin sun tafka fada da 'yan Boko Haram din lamarin da ya yi sanadin hallaka 'yan kungiyar 200 yayin da sojan Chadi 10 suka rasu baya ga wasu 20 da suka jikkata.

A jiya Lahadi ce kasashen biyu suka kutsa kai cikin tarayyar ta Najeriya da nufin fatattakar 'yan Boko Haram din da suka shafe shekaru suna tada kayar baya a kasar wanda hakan yai sanadin dubban fararen hula.