1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kan hanyar sulhunta rikicn Sudan

Abdoulaye Mamane Amadou
July 4, 2022

Gwamnatin mulkin soji a Sudan na shirin tsame hannunta daga duk wani katsalandan na siyasa da na jagoranci da zummar bar wa fararan hula damar kafa sabuwar gwamnati.

https://p.dw.com/p/4DeIw
Sudan politische Krise | Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

A wani jawabi ta kafar talabijin din kasar ne Janar Abdel Fattah al-Burhane ya bayyyana cewa za a kafa gwamnati idan aka kawo karshen tattaunawar da ake karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da  Kungiyar Tarayyar Afirka AU, bayan an rusa majalisar koli ta mulkin soja, ana kuma shirin kafa wata sabuwar da za ta kunshi sojoji da fararen hula domin tafiyar da harkokin mulki.

Kalamun shugaban na zuwa ne a yayin da masu rajin girka dimukuradiyya ke cigaba da zaman dirshen a cigaba da boren kin jinin mulkin sojan da janar al-Burhane jagoranta.

Zanga-zanga ta karade sassan kasar Sudan ciki har da fadar gwamnat ta birnin Khartum, tun bayan kifar da gwamnatin farar hula da tstinin bindiga a cikin watan Oktoban bara, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutun 112 a cewar alkaluman da likitoci da masu zanga-zanga ke fitarwa.