1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun aiwatar da juyin mulki a Burkina Faso

DattiSeptember 17, 2015

Sabon shugaban da sojojin kasar Burkina Faso suka nada a matsayin shugaban kasar Kanal Gilbert Diendere ya nisanta kansa da alaka da hambararren shugaban kasar Blaise Compaore.

https://p.dw.com/p/1GXlC
Burkina Faso Militär Soldaten Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A safiyar Alhamis ne dai aka wayi gari a kasar da juyin mulki a bayan da a ranar Larabar da ta gabata kuma sojojin kasar da ke aiki a fadar shubagan kasar suka damke shuagaban rikon kasar Micheil Kafando da Fira ministan kasar, kana da wasu ministocinsa.

Yanzu dai haka rikici a kasar ya kara barkewa duk da cewar mahukuntar kasar da suka yi ikirarin dare gadon mulkin kasar sun kafa dokar hana fita, tare kuma da bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasar ta kowanne bangare, wannan balahirar dai na zuwa ne a dai dai lokacin da zaben kasar ya rage wasu yan kwanaki a gabatar da shi. al'amarin da masu sharhi kan al'amuran dake faruwa a siyasa ke ganin matakin ya dawo da hannun agogo baya, a lokacin da jama'ar kasar ke fatan shiga sahun kasashen da zasu fara kwankwadar roman mulki irin na dimokradiyya.

Rikicin dai a ya samo asali ne a tun a ranar Laraba kasar ta shiga rudani, sakamakon wannan al'amarin da ya faru yasa dubban al'umma suka gudanar da zanga-zanga gaban fadar shugaban kasa inda jami'an tsaro suka tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da harbe harben bindiga.

Yanzu haka dai ana cigaba da zanga zanga a kasar duk da cewar sojojin da suka ayyana kafa sabuwar gwamnati sun kafa dokar hana fita, lamarin da al'ummar kasar suka yi wa matakin kunnen uwar shegu, in da suka fito don cigada da nuna bakin ciki dangane da wannan mataki.

An dai jiyo kasar harbe harben bindigogi a babban birnin kasar Wagadugu.

Sai dai kuma a nasa bangaren shugaban riko na majalisar dokokin kasar Cheriff Sy yayi kiran mutane da su kwantar da hankalinsu.

Sai dai kuma al'amarin ana tunanin ka iya daukar wani sabon salo anan gaba kadan duba ga yadda ake cigaba da yin bata kashi, kamar yadda wani dan jarida da ke sharhin al'amuran yau da kullum a kasar yayi karin haske.

Symbolbild Soldaten Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Mutane sun zauna a gidajensu tun jiya har zuwa wayewar gari sabo da ana ta harbe harben bindigogi, haka kuma an kai farmaki wasu gidajen yada labaru tare da baiwa 'yan jarida kashi da kuma fararen hula, amma kuma kusan kowa yayi Allah wadai da yadda al'amura suke tafiya a halin yanzu".

Tuni dai Majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar kasashen afrika suka bayyana rashin jin dadinsu dangane da wannan al'amari da ya faru a dai dai lokacin da kasar ke shirin dawowa bisa ga turbar bin mulkin dimokradiyya, har ma shugaban Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki moon yayi kira da a yi maza a saki shugaban gwamnatin kasar, da sauran mukarrabansa.

Shima a nasa bangaren shugaban kasar Faransa Francois Hollande yayi allah wa- dai da wannan mataki, inda shima yayi kiran da a gaggauta sakin wadanda ake tsare da su, ta yadda za a samu damar dawo da doka da kuma oda.

Yanzu dai an bayyana dokar hana fita a kasar da kuma rufe iyakokin kasar ta kowanne bangare, sakamakon tunanin da ake na rikicewar kasar, al'amarin da ya zama al'ada idan irin hakan ta faru mahukunta kan kakaba dokar hana fita

Proteste nach Militärputsch in Bukina Faso 02.11.2014
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

"Lokacin da mutane suka fara taruwa, kawai sai muka ga wata mota ta afurma tazo a guje dauke da sojoji sai kawai suka fara harbi a tsakar jama'a suna kashe mutane, duk sun rikice sojawan wai suna neman yan kungiyar Balai Citoyen wai suka ce idan sun samesu zasu hallakasu gabaki dayansu. Lalle ba kowa bane ke wannan danyan aikin sojojin RSP ne sune kawai".

Mu dai wannan abun na damunmu sosai domin mu yan kasuwa ne, kuma harkokin kasuwanci namu ya ja baya, Shi kuma wannan cewa ya ke to batun tsaro dai ynzu sai a hankali, musamman mag a wannan kasa da ta fara samun kulawa daga kasashen duniya, yanzu kuma a ce hak ata faru, domin mu har yanzu bamu gane komai ba, su wadannan mutane da a jiya suka goyu bayan al'umma sune kuma yau suka kame dukannin shugabannin kasar.