Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Mali
June 16, 2019Talla
Kakanin rundunar sojojin ya tabbatar da cewar ana ci gaba da bude wuta kan sansanin mayakan da ke iyaka da Nijar. Kasar Mali na fama da ayyukan ta'addanci tun bayan da 'yan tawaye suka mamaye yankin arewacin a shekara 2012,kafin daga bisani Faransa da sauran kawaye su sake kwato yanki.