1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Iraki na kokarin kwatar wasu yankuna daga IS

Salissou BoukariJune 12, 2015

Dakarun sojan Iraki na fama da mayakan IS a sassa daban-daban na kasar kafin isowar karin sojoji 450 daga Amirka da za su taimaka da dabarun yakar 'yan jihadin.

https://p.dw.com/p/1Fg1U
Irak US-Soldaten im Ausbildungslager Taji
Hoto: Getty Images/J. Moore

Sojonjin na Iraki dai na kokarin kwato wasu yankunan da ke hannun 'yan jihadin na IS yau shekara guda, kuma da alama ana ganin tamkar hakarsu zata cimma ruwa. Daga nasu bangare mayakan Kurdawa 'yan Peshemerga, na gurgusowa daga bangaren kudu, da kuma yammacin birnin Kirkuk, tare da samun tallafi daga hare-hare jiragen yakin kasar ta Iraki da na sojojin kawance, kuma sun tunkari wata mahadar bam ta 'yan kungiyar ta IS.

A bangaren Siriya kuwa, 'yan tawayan kasar ne suka sake samun wata galaba kan sojonjin kasar masu goyon bayan gwamnatin Bashar al-Assad, bayan da suka kwaci wani yanki mai girma na rundunar sojan saman kasar da ke Soueida.