1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Iraki na shirin kwato Mosul daga hannun IS

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2017

Sojojin gwamnatin Iraki masu samun rkkiyar jiragen yakin rundunar kawancen kasa da kasa sun kaddamar a wannan Lahadi da farmakin neman kwato tsohon birnin Mosul daga hannun mayakan Kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/2etFF
Irak Mossul
Hoto: Reuters/A.Konstantinidis

Sojojin gwamnatin Iraki masu samun rakiyar jiragen yakin rundunar kawancen kasa da kasa sun kaddamar a wannan Lahadi da farmakin neman kwato tsohon birnin Mosul daga hannun mayakan Kungiyar IS. Wannan zai zamatin zai bai wa sojojin gwamnatin Irakin damar karbe iko da illahirin birnin na biyu mafi girma a kasar ta Iraki. Dama mafi yawancin mayakan Kungiyar ta IS suna samun mafaka ne a cikinsa.

 Ana dai kallon farmakin na wannan karo a matsayin matakin karshe na kaiwa ga kwato birnin bakin dayansa da korar mayakan Kungiyar ta IS daga tungarsu inda a nan ne jagoran kungiyar Abou Bakr Al-Baghdadi ya ayyana kafa sabuwar daular Muslunci a watan Yulin shekara ta 2014. 

Sai dai babban kwamandan rundunar sojojin Irakin Abdel Ghani al-Assadi ya bayyana wannan farmaki a matsayin mai cike da hadari kasancewa mayakan na IS za su iya jan daga sosai ganin cewa tungarsu ce ta karshe, kana akwai fararen hula sama da dubu 100 da mayakan suka hana wa ficewa daga cikin birnin na Mosul domin su zamanto masu tamkar garkuwa.