Sojojin Mali sun karɓi iko da garin Ménaka.
February 12, 2013Talla
Wani babban habsan soji na Mali kanal Alaji Ag Agamu ya shaida cewar su ne da sojojin Faransa ke riƙe da garin tun sao'i 48 da suka wucce.Ya kuma ce kafin su isa a garin, mayaƙan ƙungiyar yan tawaye na MNLA sun arce, sannan kuma ya ce sun kama wasu dakarun ƙungiyar guda uku.
Tun a ranar biyar ga watan Febrairu bradan na ƙungiyar ta MNLA suke a garin na Ménaka wanda da farko ke cikin hannu masu kishin addini kafin su ficce.Wannan shi ne gari na kusan biyar da sojojin Faransa da na Mali suka karɓe daga hannu yan tawayen.Yanzu haka sojojin ƙasashen sun ƙara ƙarfafa matakan tsaro ta hanyar gudanar da bincike a kan jama'a masu yin shigi da fuci.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal