1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Thailand sun kafa dokar hana gangami

May 22, 2014

Jagoran rundunar sojin Thailand Prayut Chan-Ocha ya ce juyin mulkin ya zama wajibi domin kaucewa karin asarar rayuka da kuma lalata gine-ginen gwamnati.

https://p.dw.com/p/1C4oF
Thailand Armee verhängt Kriegsrecht 20.05.2014
Hoto: Reuters

Yanzu ta faru ta kare. Babban hafsan hafsohin sojin kasar Thailand Prayuth Chan-Ocha ya sanar da juyin mulkin ta gidan telebijin yana mai cewa.

"Kwamitin tabbatar da zaman lafiya da ya kunshi rundunar mayakan kasa da na ruwa da kuma na sama hade da rundunar 'yan sandar kasa, ya karbi ragamar iko domin tafiyar da mulkin wannan kasa daga wannan rana ta 22 ga watan Mayu."

Kifar da mulkin dai ya kawo karshen tattaunawar sulhu da aka shiga rana ta biyu a wannan Alhamis, da ke gudana a babban zauren taron rundunar ta soji a birnin Bangkok, inda hafsan sojin tun a ranar Laraba ya fara tattaunawa da wakilan sassan da ke adawa da juna, domin samun mafita daga rikicin siyasar kasar ta Thailand da ya jima cikin yamutsi, amma aka watse baran-baran.

Thailand Armee verhängt Kriegsrecht 22.05.2014
Hoto: Reuters

Shaidun ganin ido sun rawaito cewar sojoji sun yi awon gaba da shugabannin sassan da ke zanga-zangar jim kadan gabanin jawabin na babban hafsan sojin. An tsaurara matakan tsaro inda aka girke dakaru a kewayen zauren tattaunawar kuma juyin mulkin ya tafi cikin ruwan sanyi ba tare da musayar wuta ba.

Tir da juyin mulkin sojin

Pravit Rojana-Phurk sanannen dan jarida ne kuma mai sharhi a kasar ta Thailand ya yi tir da matakin da sojojin suka dauka.

"Wannan abin kunya ne. Hafsan sojojin Chan-Ocha ya kame wadanda suka je taron tattaunawar. Wannan halin rashin mutunci ne da ke nuna cewa makomar gwamnatin mulkin soji karkashin jagorancinsa ba za ta yi haske ba. Ba za a iya yarda da wannan mutumin ba. Wannan kuwa abin damuwa ne. Na damu da kamen da ake yi na gama gari na masu adawa da juyin mulkin. A maganar nan da na ke yi har yanzu akwai dubban masu zanga-zanga daga sassan biyu wato masu jajayen riguna da 'yan PDRC a kan tituna. Ba mu san abin da zai faru ko yadda za a yi da su ba."

Tuni dai sojojin suka sanya dokar hana fita da haramta gangamin mutane fiye da biyar. Sannan dokar ta-bacin da aka kafa a farkon mako za ta ci gaba da aiki. Kana an ba dukkan tashoshin telebijin da na rediyo na kasar umarnin watsa shirye-shiryen sojoji kawai.

Mutunta 'yancin jama'a na fadin albarkacin baki

Bangkok Protetse 15. Mai 2014
Hoto: Reuters

Kasashen duniya sun yin Allah wadai da juyin mulkin. Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi kira da a mayar da mulkin bin doka da oda bisa kundin tsarin mulkin kasa tare da shirya zabe kana kuma a girmama 'yancin al'ummar Thailand na fadin albarkacin baki.

Ita ma hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa ga juyin mulkin tana mai cewa dokokin soji da aka kafa na zama barazana ga 'yancin jama'a na bayyana ra'ayinsu da yin gangami da kuma kariya daga tsare su ba bisa ka'ida ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu