1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Solana na yunkurin sasanta Duniyar Musulmi da kasashen Yamma

February 15, 2006

Rikicin da ya barke, tare da zanga-zangar da aka yi ta gudanarwa a duniyar musulmi, dangane da batancin nan da aka yi wa addinin islama ta hanyar siffanta annabi Muhammadu (s.a.w) da hotunan zane, shi ne dalilin ziyarar baya-bayan nan da babban jami'in Kungiyar Hadin Kan Turai mai kula da batutuwan harkokin waje, Javier Solana, ya kai a kasashen Saudiyya da Masar.

https://p.dw.com/p/BvTo
Javier Solana (hagu) yayin ganawarsa da shugaba Hosni Mubarak na kasar Masar, a birnin al-Kahira.
Javier Solana (hagu) yayin ganawarsa da shugaba Hosni Mubarak na kasar Masar, a birnin al-Kahira.Hoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

A rangadin diplomasiyya da yake kaiwa a yankin Gabas Ta Tsakiya, babban jami’in Kungiyar Hadin Kan Turai mai kula da batutuwan da suka shafi harkokin waje, Javier Solana, ya yi ta nanata cewa, bai kamata a ci gaba da samun baraka tsakanin nahiyar Turai da duniyar musulmi ba, dangane da zanen batancin nan ga addinin islama da ke siffanta kamannin annabi Muhammadu, tsira da maincin Allah su tabbata a gare shi, wanda aka fara bugawa a cikin wata jaridar kasar Denmark. A ziyarar da ya kai a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, jami’in ya gana ne da babban sakataren Kungiyar Musulmi ta Duniya, Ekmeleddin Ihsanoglu, sa’annan a jiya talata kuma, ya yi shawarwari da shugaba Hosni Mubarak da ministan harkokin wajen kasar Masar, Ahmed Abdul-Gheit, a birnin Al-kahira. Game da yunkurin sasantawa da yake yi dai, Javier Solana, ya bayyana cewa:-

„Al’amuran da suka wakana a kwanakin baya dai, wato wani kira ne na gangami, wanda ke jaddada mana irin muhimmancin da tuntuba da kusantar juna ke da shi tsakaninmmu.“

Kawo yanzu dai, fiye da mutane 10 ne suka rasa rayukansu a zanga-zanagar da aka yi ta yi a yankuna daban-daban na duniya, dangane da zanen batancin da aka yi wa addinin islama. Wannan dai ba abin da ya kamata a zauna a yi shiru a yi ta kallon yadda al’amura ke ta kara habaka ba ne, inji Solana. A nasa ganin, duk da hauhawar tsamarin da aka samu, akwai kuma alamun cim ma shawo kan matsalar:-

„Ba za a iya dai cewa, ba a dau wasu matakan tinkarar matsalar ba. Mun yi ta kokarin shimfida wata gada ta tabbatad da yarda da juna tsakaninmu.“

To sai dai, wannan yunkurin tabbatad da yarda da juna, kamar yadda Solanan ke nanatawa, bai wadata ba, a ganin mahukuntan Saudiyya da kuma na Masar. Suna neman fadada duk wasu matakan da za a dauka ne, su hada da zartad da kuduri a Majalisar Dinkin Duniya, inda za a bukaci duk kasashe mambobin majalisar da su hukuntad da duk masu wulakanta addinai da manzanninsu. Kamar yadda ministan harkokin wajen Masar, Ahmed Abul-Gheit ya bayyanar:-

„Kasashe dari da daya ne suka goyi bayan kundin wannan kudurin, sa’annan 54 kuma suka juya masa baya. Na tattauna a kan wannan batun da Solana. Ina kuma kyautata zaton cewa, za a iya cim ma daidaito tsakanin duniyar musulmi da kasashen Yamma, wajen kago hanyoyin da nan gaba, za a iya bi ta kansu, wajen magance irin wadannan matsalolin.“

Shi dai babban jami’in diplomasiyya na Kungiyar Hadin Kan Turan, Solana, bai fito fili ya goyi bayan shawarar zartad da kuduri a Majalisar Dinkin Duniyar ba. Amma ya bayyana wa abokan huldarsa a Masar cewa:-

„Muna girmama duk addinai, wato addinin islama da sauran duk addinai. Wannan na daya daga cikin jigajiganmu na cewa mu girmama addinan da ma ba namu ba. Tasrin nuna hakuri da juna kuma na muhimmanci. Abin da ke nufin girmama junanmu.“

Tun cikin watan Oktoban shekarar bara ne dai, ministan harkokin wajen Masar Ahmed Abul-Gheit, ya tuntubi jami’an biranen Copenhagen da Brussels game da batun zanen batancin. Amma babu wanda ya dauke shi da muhimmanci. A halin yanzu kuwa, shwarar da ya gabatar kuma yake neman a yarje a kanta ne, zartad da kuduri, wanda a ganinsa, zai hana hauhawar tsamari da tabarbarewar al’amura nan gaba:-

„Wajibi ne mu cimm ma fahimta, ta yadda babu wanda zai afka wa wani, kuma za a daina duk wani zargai tsakanin juna.“

Duk jami’an biyu dai, wato Abul Gheit da Solana, suna kira ne ga hakuri da juna, don cim ma fahimta da kuma kyakyawan zaman cude ni in cude ka cikin lumana.