1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma taron Majalisar Tarayyar Turai

July 1, 2014

A wannan Talatar ce sabuwar Majalisar Tarayyar Turai ke soma zaman taron ta, inda a cikin wannan zama ne, 'yan Majalisar zasu zabi kakakin Majalisar.

https://p.dw.com/p/1CTA9
Hoto: DW/S. Huseinovic

Matsin kaimin da 'yan Majalisun masu kyamar kungiyar ta Tarayyar Turai, da suka samu karin karfi a zaben da ya gudana na ran 25 ga watan Mayu da ya gabata ke yi, na tilasta wa Jam'iyyu masu ra'ayin hadin kan na Turai kama jikin su domin yin wani abin azo a gani.

Ana sa ran cewar, za'a sake zaben dan Jam'iyyar Social-Democrate na Jamus Martin Schulz, a matsayin shugaban Majalisar, a wani wa'adi na shekaru biyu da rabi, dangane da yarjejeniya da aka cimma tsakanin bangarori, sai dai kuma ana sa ran tsayawar wasu 'yan takara uku a zagaye na farko, da suka hada da dan Conservative, Sajjad Karim na Britaniya, da Pablo Iglesias na Spain, da kuma Ulrike Lunacek na Austria.

Sai dai tuni masu lura da al'ammura ke ganin cewar, idan har Majalisar ta Tarayyar Turai na son kare mutuncinta, to wajibi ne a samu hadin kan dukkanin masu rajin kare demokaradiyya a zauran Majalisar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu