1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma zaman shari'ar shugabar Koriya ta Kudu

Suleiman Babayo
January 3, 2017

Kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu ta fara zaman sauraron badakalar siyasa da ta janyo aka tsige Shugaba Park Geun-Hye daga kan karagar mulki domin bayyana matsayinta na karshe kan makomar shugabar. 

https://p.dw.com/p/2VCZw
Südkorea Prozess Choi Soon-sil
Hoto: picture-alliance/AP Photo

 

Zaman sauraron bangaorin da kotun tsarin mulkin kasar ta Koriya ta Kudu ta fara a wannan Talata kamar yadda aka yi tsammani Shugabar Park Geun-Hye ba ta cikin wadanda suka halarta, kuma zargi cin hanci da amfani da karfi da hanyar da ta saba doka kan hada baki da wata kawarta Choi Soon Sil suka saka majalisar dokoki ta dauki matakin tsige shugabar, wacce ta musanta zargin yin ba dai dai ba, amma ta ba da hakuri.
A cewar shugaban kotun tsarin mulkin Park Han-chul, za su tabbatar da adalci:


"Kotun tsarin mulki za ta ci gaba da kasancewa mai adalci wadda ba ta goyon bayan kowani bangare, za mu yi kokarin sauraron kowa ba tare da nuna son-kai ba."

Ita dai majalisar dokoki da ta kada kuri'ar tsige shugbar ta Koriya ta Kudu, ta nuna rashin jin dadi kan yadda Shugaba Park Geun-Hye ta kaurace wa zaman kotun na wannan Talata, kamar yadda shugaban kwamitin shari'a na majalisar dokokin kasar Kwon Seong Dong ke cewa:

Südkoreas Parlament entscheidet über Amtsenthebung von Präsidentin Park
Hoto: picture-alliance/dpa/Yonhap

 

"Kamar yadda aka gani a wannan zama, an jinkirta sauraro saboda rashin wadda ake zargi"

Bayan rashin halartar zaman, alkalan kotun guda tara sun dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis mai zuwa 5 ga wannan wata na Janairu, inda aka tsara wasu makarabanta da wadanda suka taba aiki tare da shugabar za su bayar da bahasi. Kuma a cewar Kwon Seong Dong shugaban kwamitin shari'a na majalisar dokoki, shugabar kadai za ta iya warware zare da abawa, sannan ya ce ba ganawa da 'yan jarida ba ne zai wanke shugabar:

 

"Ginshikin saboda Park ce za ta iya warware komai a kotu. Ba daidai ba ne magana da 'yan jarida a wajen kotun. Matsayinmu shi ne Park ta daina ganawa da 'yan jarida domin wanke kanta."

Südkorea Verfassungsgericht Choi Soon Sil
Hoto: picture-alliance/dpa/Yonhap

Amma har yanzu akwai rashin tabbas kan Shugaba Park Geun-hHye za ta halarci zaman kotun tsarin, saboda lauyan da yake kare ta, Lee Joong-hwan ya ce babu wani dalilin haka:

 

"Abin da nake tsammani shi ne ba za ta halarci zaman kotun ba, sai dai karkashi wani yanayi na musamman."

Tilas kotun tsarin mulkin ta Koriya ta Kudu ta tantance cikin watanni shida ko Shugaba Park Geun-Hye ta yi sallama da madafun iko har abada, ko kuma a mayar da ita kan matsayin idan babu laifin da aka tabbatar ta aikata. Ita dai Koriya ta Kudu ta fada cikin rikicin siyasa tun lokacin da aka bankado abin kunya da ake zargin wasu manyan jami'an gwamnati suna neman abin duniya ta hanyar amfani da mukamunsu.