1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya ta sake tsunduma cikin fitina

April 19, 2013

Hare haren bama bamai da kungiyar Al-Shabaab ta kai a birnin Mogadishu sun nuna a fili cewa har yanzu kungiyar na iya aiwatar da harin ta'adanci a duk lokacin da ta so.

https://p.dw.com/p/18JLu
Hoto: Mohamed Abdiwahab/AFP/Getty Images

Bari mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a babban labarinta mai taken "Tsoro ya dawo" ta mayar da hankali a kan halin da ake ciki a Somaliya tana mai nuni da hare haren bam guda biyu da aka kai a babban birnin kasar wato Mogadishu wanda ta ce ya nuna cewa ko kadan ba a ci kungiyar Al-Shabaab da yaki ba sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

"Sakon dai a bayyane yake wato jefa gwamnatin Somaliya da duk mai tallafawa domin sake gina kasar, cikin fargaba. Kasancewa hare haren da kuma musayar wutar da aka yi duk sun rutsa da 'yan kasar da kuma kungiyoyin ba da agaji dake aiki a birnin na Mogadishu. Shugaba Hassan Sheikh Mohamoud yayi kokarin ceto sunan kasarsa dake kan hanyar samun daidaituwar al'amura, inda ya bayyana jerin hare haren da cewa ba komai ba ne illa wata alamar rudu ta 'yan ta'adda wadanda suka rasa tungarsu kuma ke kara janyewa daga sassan kasar ta Somaliya. Hare haren dai na ranar Lahadi da suka halaka mutane akalla 30 sannan wasu 50 suka jikata, sune mafi muni a Mogadishu tun bayan da dakaraun tarayyar Afirka suka fatattaki sojojin Al-Shabaab daga birnin a watan Agustan shekarar 2011."

Bildergalerie Somalia Sicherheitslage Shebab
Hoto: Mohamed Abdiwahab/AFP/Getty Images

Al-Shabaab ka iya kaddamar da hari a kowane lokaci

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci kan halin da ake ciki a Somaliya. A wani labari mai taken 'yan ta'addar Somaliya sun fara kunno kai sai ta ce ci gaba da cewa.

"Bayan mummunan harin ta'addanci da aka kai birnin Mogadishu tun bayan korar Al-Shabaab, hukumomi sun kame mutane da dama da ake zargi da hannu a wannan ta'asa. Sai dai harin ya nuna cewa masu tsattsauran ra'ayin sun samu nasarar sauya dubarunsu don dacewa da halin da ake ciki. Su kuma a nasu bangaren dakarun tsaron Somaliya sun fadada tsintiri a Mogadishu in da suka kame daruruwan matasa ba ji ba gani. A cewar jaridar harin mafi muni tun bayan fatattakar Al-Shabaab daga Mogadishu a shekarar 2011, ya nuna a fili cewa a kowane lokaci sojojin sa kan ka iya aiwatar da barazanarsu wato sanya tsoro da fargaba a tsakanin al'umma sannan su jefa gwamnatin da a da ma take tangal-tangal cikin rudani."

Tsugune ba ta kare ba a Bangui

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung a wannan makon ta mayar da hankali ne a kan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana mai cewa: 'Yan tawaye sun farma sojojin sa kai, har yanzu tsugune ba ta kare ba a birnin Bangui, sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

Zentralafrikanische Republik Seleka Rebellen April 2013
Hoto: AFP/Getty Images

"Bisa ga dukkan alamu sabbin mahukuntan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kasa shawo kan mawuyacin halin da ake ciki, bayan da a farkon wannan mako gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawayen Seleka da ta karbi ragamar mulki a Bangui ranar 24 ga watan Maris, ta sanar da zuwan sojoji kimanin 1000 daga kasashe makwabta domin abin da ta kira tabbatar da tsaro a babban birnin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Fomac ta kunshi sojojin Kamaru, Gabon da kuma Chadi. Hade da mayakan Seleka za su rika yin sintiri na hadin guiwa a birnin na Bangui wanda ke fama da tashe tashen hankula tsakanin 'yan tawaye da wasu sojojin sa kai magoya bayan tsohon shugaban kasa Francois Bozize."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe