1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Spain ta ware kudade ga ayyukan jin kai a Gaza

February 5, 2024

Spain ta sanar da ware tallafin gaggawa na makuden kudade ga hukumar UNRWA domin ceto ayyukan jin kai da ke neman tabarbarewa a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4c4mM
UNRWA in Gaza | Hilfswerk der Vereinten Nationen
Hoto: Amr Abdallah /REUTERS

Kasar Spain ta sanar da ware tallafin gaggauwa na Yuro miliyan 3,5 ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin Falasdinu, wacce ke fuskantar barazanar katsewar tallafi daga kasashe da dama bayan zargin cewa da hannun ma'aikatanta a harin da Hamas ta kai wa Isra'ila.

Karin bayani: Rashin ba da tallafi wa UNRWA zai haifar da mummunar sakkamako a Gaza

Yayin da yake sanar da wannan tallafi, ministan harkokin wajen Spain José Luis Albares ya ce akwai damuwa mai matukar hadari a makonnin masu zuwa idan ayyukan jin kai suka tabarbare a zirin Gaza.

A cewar babban jami'in diflomasiyyan Tarayyar Turai Josep Borrel, tallafin da aka katse wa hukumar a halin yanzu ya kai dalar Amurka miliyan 440 kusan rabin kudaden da take bukata a wannan shekarar ta 2024.

Dama dai a cikin kungiyar Tarayyar Turai, kasar Spain ta kasance mai adawa da matakin Isra'ila tun bayan farmakin da ta kaddamar kan kungiyar Hamas da wadansu kasashe ciki har da Amurka suka bayyana a matsayin ta 'yan ta'adda domin daukar fansa kan harin ranar bakwai ga watan Otoban bara.