1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta ce zata karbi ragamar kiyaye zaman lafiya a Dafur

June 27, 2006
https://p.dw.com/p/BusX

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yace mai yiwuwa ne kasar ta karbi ragamar ayyukan kiyaye zaman lafiya a yankin Dafur mai fama da rikici. Ya baiyana hakan ne a jiya a matakin kara nuna rashin amincewa da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya. Albashir yace Sudan a shirye take ta karbi shaánin gudanarwar kiyaye zaman lafiyar idan kungiyar gamaiyar Afrika ta sauke nauyin da aka dora mata na wannan aikin . Turjiyar da Sudan ta nuna kan tura sojojin ya haifar da rashin jituwa tsakanin gwamnatin da majalisar dinkin duniya.