1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Sabon rikici ya barke

Zainab Mohammed AbubakarJune 29, 2016

wajen mutane dubu 70 ne suka tsere saboda kazamin fada da ke gudana a yankin Arewa maso Yammacin kasar, kana gawarwaki na cigaba da mamaye tituna.

https://p.dw.com/p/1JGQB
Südsudan Flüchtlingslager Yida
Hoto: DW/L. Wagenknecht

Gwamnatin Sudan ta Kudun dai ta zargi wata sabuwar kungiyar fafutuka data bulla a kasar da sabbin tashe tashen hankulan, kasar da mayakan sakai ke ci gaba da cin karensu babu babbaka, bayan da gwamnatin wucin gadi ta cimma kawo karshen rikicin madafan iko na sama da shekaru biyu tsakanin shugaba Salva Kiir da mataimakinsa deputy Riek Machar, a watan Afrilu.

Kungiyar litocin kasa da kasa da ake kira"Na gari na kowa" ta ce tun daga ranar Juma'a kawo yanzu dai, mutane wajen dubu 70 suka tsere daga garin Wau, dubu 10 daga cikinsu na samun mafaka a sansanin Majalisar Dunkin Duniya, a yayin da wasu ke ci gaba da gudu.

Kazalika wajen mutane 334 ne ke samun jinya saboda raunukan harsashin bindiga da fyade da wasu cututtuka.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu kawo yanzu, a yayin da sama dan miliyan biyu suka tsere daga matsugunnensu a jaririyar kasar ta Sudan ta Kudu, tun bayan barkewar rikicin na madafan iko a watan Disamban 2013.