1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu ta yi fatali da taswirar zaman lafiya

Suleiman BabayoAugust 18, 2015

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi watsi da matsin lamba da jami'an diplomasiya kan saka hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawaye

https://p.dw.com/p/1GHFR
Südsudan-Verhandlungen vorerst gescheitert
Hoto: Reuters/Jok Solomun

A wannan Talata gwamnatin Sudan ta Kudu ta caccaki kunshin yarjejeniyar zaman lafiya da aka bukaci ta rantaba hannu a kai, domin kawo karshen yakin basasan kasar. Ministan yada labarai na kasar ya ce yarjejeniyar ba za ta ceci 'yan Sudan ta Kudu ba.

Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Sudan ta Kudu sun nemi bangarorin da ke rikici da juna su ajiye takama da tunkaho, domin amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya, kwana guda bayan Shugaba Salva Kiir ya yi turjiya kan saka hannu a yarjejeniyar da za ta kawo karshen rikicin kasar na watanni 20. Shugaba Kiir ya koma gida daga kasar Habasha inda aka tattauna shirin na zaman lafiya.

Kiir ya nemi kwanaki 15 domin ya tattauna kan yarjejeniyar tare da kauce wa matsin lamba daga kasashen yankin kan wa'adin da aka gindaya a wannan Litinin da ta gabata. Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda ya nunar da cewa akwai matukar wahala a samu abin da ake bukata karkashin irin wannan yanayi na Sudan ta Kudu.

A shekara ta 2011 Sudan ta Kudu da balle daga Sudan, sannan yan fada cikin yakin basasa a watan Disamba na shekara ta 2013.