1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta yi kira ga Au ta kwashe dakarun ta daga Darfur

September 4, 2006
https://p.dw.com/p/Buki

Ƙasar Sudan ta yi kira ga ƙungiyar tarayya Afrika, ta janye dakarun ta daga yankin Darfur, kamin 30 ga watan satumber.

Wannan sanarwa ta biwo bayan ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Dunia,ta rataba hannu kan sa, na tura rundunar shiga tsakani ta ƙasa da ƙasa, wace zata maye gurbin dakarun AU a Darfur.

Ba da wata wata ba, Sudan ta sa ƙafa ta shure ƙudurin.

Sanarwar da ƙungiyar taraya Afrika ta hiddo, ta ce gwamnatin Sudan, ta jibge dubunan sojoji a wannan yanki, wanda ke ci gaba da farautar yan tawayen da su rataba hannu ba, akan yarjejeniyar zaman lahia, da aka cimma, a birnin Abuja na Taraya Nigeria.

Kakakin ministan harakokin wajen ƙasar Sudan, Jamal Ibrahim, ya ce Sudan ba amince ba, da matsayin taraya Afrika, na bada goya baya ga Majalisar Ɗinkin DUnia, ta fannin aika dakarun ta, a Darfur