1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga- zangar 'yan adawa a Sudan

Abdourahamane Hassane
January 11, 2019

Kungiyoyi masu fafutuka a Sudan sun yi  kiran wasu sabbin borai bayan sallah Juma'a a garuruwa da dama na kasar.

https://p.dw.com/p/3BOFd
Sudan Proteste in Omdurman
Hoto: Reuters/social media/Haitham Seo

A cikin wata sanarwa da hadin gwiwar kungiyoyin suka bayyana sun ce za su yi mako daya jere na gangami a ckin garuruwa da kauyuka domin tilasta wa shugaba Omar al-Bashir yin marabus. Yau kusan makonnin uku ke'nan da gwamnatin ta Sudan take fuskantar borai mafI muni tun daga shekara ta 1989 lokacin da Al Bashir ya karbi mulki. Kungiyar kare hakin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce mutane 40 suka mutu a zanga-zangar da farko ta neman a rage frashin kudin biredi ce kafin ta rikide ta koma ta siyasa.