1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria ta tsame kan ta daga zargin kisan Wali Eido

June 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuIp

Syria ta yi kakkausar suka tare da Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa wani dan majalisar dokokin Lebanon Walid Eido a wani harin bom a birnin Beirut a ranar larabar data wuce. Gwamnatin ta Syria ta kuma musanta zargin cewa tana da hannu a kisan. Dubban jamaá da suka halarci janaízar sun yi ta furta kalamai na sukar lamirin Syria a yayin da suke kan hanya zuwa wata makabarta a birnin Beirut inda aka binne mamacin. Aminan ɗan majalisar sun zargi Syria da shirya kisan. Daga watan Fabrairu na shekarar 2005 da aka kashe tsohon P/M Lebanon Rafik al-Hariri ya zuwa yanzu, wannan shine karo na bakwai da aka kashe mashahuran mutane waɗanda ke adawa da gwamnatin Syria. Maáikatar harkokin wajen Syria a birnin Damascus tace wasu yan Lebanon na yaɗa farfaganda domin a bata mata suna.