1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar Mali

December 26, 2012

Rikicin da ya ɓarke a yankin arewacin ƙasar Mali ya saka mutane da dama cikin halin zaman kashe wando.

https://p.dw.com/p/1796y
Fighters from Islamist group Ansar Dine stand guard as they prepare to hand over a Swiss female hostage for transport by helicopter to neighboring Burkina Faso, at a designated rendezvous point in the desert outside Timbuktu, Mali Tuesday, April 24, 2012. Two main groups now appear to be competing to govern northern Mali: Ansar Dine, which wants to see Sharia law brought to Mali, and separatist rebels who already have declared an independent state. (Foto:AP/dapd)
Hoto: dapd

Sannu a hankali dai mummunan tasirin da rikicin yankin arewacin Mali ya janyowa tattalin arzikin ƙasar na yaɗuwa zuwa sauran ƙasashen Afirka da dama. Hakan kuwa ya afku ne bayan da ofisoshin jakadancin ƙasashen ƙetare daban- daban suka gargaɗi al'ummomin su da su ƙauracewa zuwa ƙasar, wadda gabannin rikicin 'yan tawaye a yankin arewaci ke zama dandalin 'yan yawon buɗe ido a yankin yammacin Afirka.

Bayan da 'yan tawayen da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qa'ida suka karɓe iko da yankin arewacin Mali, ƙungiyoyin ƙetare da dama ne suka dakatar da gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar, kana 'yan Mali da dama ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin aikin yi, baya ga ƙaruwar farashin kayayakin abinci da na anfanin yau da kullum, da ma na sana'oin hannu irin kafinta:

Aboukar Sinayoko yana shan iska ne a gaban shagon aikin kafintarsa, inda ya ke shan shayi, kuma a bisa al'ada ma'aikata 20 ne ke yin aikin samar da kujeru da sauran kayayyakin anfani a gida ga masu buƙata a birnin Bamako. Sai dai a cikin watannin baya bayannan,ya sallami 18 daga cikin ma'aikatan nasa saboda rashin aiki a yanzu. Aboukar, wanda ke da 'ya'ya 12 dai yana cikin damuwa domin kuwa ya gaza biya musu kuɗin makaranta, ga kuma bashin kuɗin wutar lantarkin da ke kansa. Sannan kuma bai san ranar ganin sauyi ba:

Ya ce :Rikicin da ke faruwa a yankin arewacin Mali yana janyo matsaloli da dama anan. A duk lokacin da aka samu rikici a kasar mu, mu Iyayen da ke da 'ya'ya masu yawa muna fuskantar matsaloli da dama domin harkokin kasuwanci ba sa tafiya yanda ya dace. Abinda nake fata shi ne kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a arewacin Mali. Gaskiya abinda nake fata kenan.

40 year old mother of three, Dalla Sininta, sits in her empty restaurant in Bamako. It's lunchtime and she hasn't seen a customer all day. / Dalla Sininta, 40, Mutter von drei Kindern, sitzt in ihrem leeren Restaurant in Bamako. Obwohl es Mittagszeit ist, hat sie den ganzen tag noch keinen Kunden gesehen. Bild: Tamasin Ford 28/11/2012 13.44, Bamako, Mali
Gidan abinci babu masayaHoto: Tamasin Ford

A kusa da shagon aikin kafintar Aboukar dai akwai wasu telolin da ke gudanar da sana'arsu, amma biyu daga cikin su ne kawai suka iya buɗe shagunan su domin ƙarancin aiki duk kuwa da cewar gabannin rikicin arewacin Mali, wannan lokaci na shekara ne 'yan ƙasar ke yawaita yin aure, tare da ɗinke-ɗinken sanyawa a bukukuwan, amma tunda ana fama da rikici, mutane a su da kuɗin kashewa, abinda kuma ke haddasa koma baya ga irin wannan sana'ar. Dalla Sinita da ke zama asalin mai shagunan ɗinkin, ta ce tasirin rikicin bai tsaya a gareta kaɗai ba :

Ta ce :A nahiyar Afirka mutum yakan tallafawa iyayensa, amma idan kasuwanci bai tafiya, to, abin kunya ne kuma abin takaici ne a gareni.

Hakane dai labarin yake ga masu sana'ar hotel-hotel, waɗanda ke sallamar ma'aikatan su tunda babu 'yan yawon buɗe idon da ke zuwa ƙasar. Kai! Hatta masu tukin kwale-kwale a garuruwan Mopti da Gao domin jigilar 'yan yawon buɗe zuwa birnin Timbuktu, mai cike da abubuwan tarihi na kokawa game da rashin abokan hulɗa a watannin baya bayannan, kamar yanda Modibo Ballo ɗaya daga cikin masu sana'ar ya faɗi:

Ya ce : Lokaci na ƙarshen da na samun fasinja shi ne a watan Faburairu. Tun daga wancan lokacin, ba 'yan yawon buɗe idon da suka zo nan.

Bildbeschreibung: Malische Flüchtlinge in Burkina Faso Schlagworte:Mali, Flüchtlinge, UNHCR, Burkina Faso Überschrift: Malische Flüchtlinge in Burkina Faso Fotograf: Peter Hille Ort: Sag-Nioniogo, Burkina Faso Thematischer Zusammenhang: Malische Flüchtlinge im UNHCR-Flüchtlingslager in Sag-Nioniogo, Burkina Faso
Matasa na zaman daraHoto: DW/Peter Hille

Rikicin na Mali dai ya tilastawa masu sana'oi zama a ƙarƙashin bishiyoyi kawai - tunda ba su da abin yi. A cewar ministan kula da harkokin sana'oin hannu da yawon buɗe a Mali Ousmane Rhissa, matsalar ta yi tsanani sosai:

Ya ce :Mummunan tasiri ne rikicin ya janyowa kamfanonin dake harkar yawon buɗe ido. domin tunda babu 'yan yawon buɗe idon da ke zuwa, babu kuɗaɗen shiga da ake samu kenan.

Kasancewar yawon buɗe ido ne babbar hanyar samun kuɗin shiga ga Mali, rikicin ƙasar ya sa kusan kowa ne ke ji a jikinsa.

Mawallafi:Saleh Umar Saleh
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani